logo

HAUSA

UAE ta musanta ba da makamai da harsasai ga bangarorin da ke rikici da juna a Sudan

2023-08-14 10:23:18 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta yi watsi da ikirarin cewa ta baiwa bangarorin da ke yaki da juna a kasar Sudan makamai da alburusai.

Kamfanin dillancin labaran WAM ya rawaito daga jami'ar ma'aikatar harkokin wajen kasar Afra Al Hameli cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta tare da wani bangare a rikicin da ya dabaibaye kasar Sudan, kuma tana neman kawo karshen rikicin, da kira da a mutunta ‘yancin kasar Sudan.

Jami’ar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayyana hakan ne bayan da jaridar Wall Street Journal ta ruwaito a makon da ya gabata cewa, an gano akwatunan makamai da harsasai a cikin wani jirgin dakon kaya na UAE da ya isa Uganda a farkon watan Yuni, maimakon kayayyakin agaji ga ‘yan gudun hijirar Sudan, kamar yadda bayanan jirgin suka nuna.

Afra Al Hameli ta ce Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta samar da makamai da harsasai ga ko daya daga cikin bangarorin da ke rikici da juna a Sudan ba tun bayan barkewar rikicin a watan Afrilu.

Ta kara da cewa, kasarta za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga duk wani yunkuri na samar da tsaro a Sudan da kuma inganta zaman lafiya da wadatarta har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. (Yahaya)