logo

HAUSA

Mutane 10 sun rasu sakamakon ruftawar tsohon masallacin birnin Zazzau na jihar kaduna dake arewacin Najeriya

2023-08-13 16:45:41 CMG Hausa

A kalla mutane 10 ne suka rasu, lokacin da rufin tsohon masallacin birnin zazzau na jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ya rufta. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna Mohammed Jalige, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, wani bangare na rufin masallacin ya fado kan masu ibadar ne a ranar Juma’a, yayin da suke sallah La’asar, kuma bayan aukuwar ibtila’in, an zakulo gawawwakin mutane 10 daga baraguzan ginin, baya ga wasu mutane 25 da suka ji raunuka, ciki har da 7 da raunukan su suka tsananta.

Mohammed Jalige, ya ce an riga an kammala aikin ceto, an kuma fara gudanar da cikakken bincike game da lamarin.

A nasa bangare kuwa, sarkin Zazzau Ahmed Bamalli, ya shaidawa ‘yan jarida cewa, kwana guda kafin aukuwar lamarin, sun lura wani bangaren bangon masallacin ya fara tsagewa, suna kuma shirin baiwa tawagar injiniyoyin gini umarnin gudanar da aikin gyaran masallacin ne kuma wannan ibtila’i ya auku.    (Saminu Alhassan)