logo

HAUSA

Dan siyasar Japan yana son sake jefa al’ummar Taiwan cikin mawuyacin hali

2023-08-12 15:35:44 CMG Hausa

Kwanan baya mataimakin shugaban jam’iyyar LDP ta kasar Japan kuma tsohon firayin ministan kasar Aso Taro ya kai wa yankin Taiwan na kasar Sin ziyara, inda ya bayyana cewa, ya dace yankin Taiwan ya shirya yin yaki da babban yankin kasar Sin, lamarin da ya gamu da suka daga bangarori daban daban. Ra’ayoyin jama’a na tsibirin Taiwan na zargin cewa, Aso Taro bai nemi gafara daga al’ummar Taiwan sakamakon mulkin mallakar Japan a baya ba, amma yana ingiza al’ummar yankin da su shirya yin yaki, ainihin yunkurinsa shi ne sake jefa su cikin mawuyacin hali.

Hakika Aso Taro ya taba yin tsokacin da bai dace ba sau tari, misali ya taba bayyana cewa, “Kasashen Amurka da Japan za su kare Taiwan tare” a shekarar 2021, kuma ya sake bayyana a watan Yunin bana cewe, “Taiwan yana da muhimmanci matuka ga Japan”. Ana iya cewa, ziyarar da ya yi a Taiwan a wannan karo ta nuna wasu manufofin gwamnatin kasar Japan wato musunta abubuwan da suka faru a tarihi da kuma kin yarda da gyara kura-kuran da suka aikata a baya. (Jamila)