logo

HAUSA

Kasar Sin na fatan Philippines za ta yi abin da ya dace kan lamarin teku

2023-08-12 15:54:13 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya Juma'a, bayan arangama da aka yi a Ren'ai Jiao a baya-bayan nan cewa, kasar Sin na fatan Pilippines za ta gaggauta yin abin da ya dace don daidaita harkokinta a tekun kudancin Sin,

A yayin ziyararsa a Singapore da Malaysia, Wang wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS ya bayyana cewa, kasar Sin tana son daidaita sabanin dake tsakaninta da Philippines ta hanyar tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Ya bayyana fatan cewa, bangaren Philippine zai mutunta yarjejeniyar da aka cimma a baya, da kuma kiyaye amincewar juna da aka samu ta hanyar kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu, da fahimtar kasar Sin ta hanyar tattaunawa, domin samun mafita dangane da harkokin teku yadda ya kamata.

A jiya Juma'a har ila yau, firaministan kasar Malaysia Anwar Ibrahim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a birnin Penang na kasar Malaysia, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin zurfafa hadin gwiwarsu da yin kokarin samun nasara tare. (Yahaya)