logo

HAUSA

Shugaban ’yan sandan Najeriya ya nemi hadin kan sarakunan kasar wajen yaki da ayyukan ta’addanci a tsakanin matasa

2023-08-12 14:58:59 CMG HAUSA

 

Babban sefeton ’yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce wajibi ne sai sarakuna sun bayar da hadin kan da ya kamata za a samu al’umma mai cike da tarbiya da sanin ya kamata a matsayinsu na iyaye.

Ya bayyana hakan ne jiya Juma’a 11 ga wata lokacin da ya ziyarci mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa, ya ce tsarin shigo da jama’a cikin ayyukan ’yan sanda na tabbatar da tsaro, tsari ne da yake bukatar tallafin duk wani dan kasa na-gari.

Daga Tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.