logo

HAUSA

Sin da Singapore za su ciyar da alakarsu gaba

2023-08-11 19:08:50 CMG Hausa

Firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ke ziyara a kasar Singapore a yau Juma’a, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin ciyar da alaka da hadin gwiwa dake tsakaninsu gaba.

Wang, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS, yana ziyarar kwanaki biyu a kasar, matakin farko na rangadinsa a kasashe uku wanda zai karasa a kasashen Malaysia da Cambodia.

Wang ya kuma gana da mataimakin firaministan kasar Singapore Lawrence Wong a wannan rana. (Yahaya)