logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin a Ghana ya bude cibiyar bayar da visa

2023-08-11 11:31:16 CMG Hausa

Ofishin jakadancin kasar Sin a Ghana, ya kaddamar da sabuwar cibiyar neman visa a Accra babban birnin kasar, da zummar saukaka shirye-shiryen tafiya ga ’yan kasar dake son zuwa kasar Sin.

Yayin bikin kaddamar da cibiyar, jakadan Sin a Ghana Lu Kun ya ce, samar da cibiyar ya zama wajibi bisa la’akari da sa ran da ake na samun karuwar mutanen Ghana dake sha’awar ziyartar kasar Sin.

Ya kara da cewa, musaya ta fuskar tattalin arziki da ma cinikayya tsakanin kasashen biyu na kyautatuwa, inda Sin ke zaman babbar abokiyar cinikayya ga kasar Ghana.

A nata bangare, mataimakiyar ministan harkokin wajen Ghana, Mavis Nkansah Boadu ta yi maraba da bude cibiyar. Tana mai cewa tana alamta wani gagagrumin ci gaba a dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana.

Ta ce kasarta na sane da muhimmancin dake tattare da karfafa dangantaka da Sin da ma kara kyautata musaya tsakanin jama’arsu. Tana mai cewa, cibiyar za ta taimaka wajen habaka bangarorin bude ido da kasuwanci da hadin gwiwa a bangaren ilimi da musayar al’adu tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)