logo

HAUSA

Taron BRICS na 2023 zai kalubalanci babakeren kasashen yamma da takardar kudi ta dala

2023-08-11 11:33:02 CMG Hausa

Ana sa ran taron BRICS karo na 15 da zai gudana nan gaba kadan a wannan wata a kasar Afrika ta Kudu, ya kawo daidaito ga tsarin tafiyar da harkokin duniya da tunkarar babakeren kasashen yamma.

Carlos Maria Correa, daraktan zartaswa na cibiyar bincike da nazarin manufofin kasashe masu tasowa ta South Centre ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A cewarsa, ajandar taron zai mayar da hankali ne ga kokarin rage karfin takardar kudin dala da ya yi wa hada-hadar duniya babakere da kuma fadada kungiyar.

Ya ce wani abu mai muhimmanci da ya kamata BRICS ta yi la’akari da shi, shi ne tsarin tafiyar da harkokin duniya. Yana mai cewa, akwai bukatar sauya tsarin da ake kai a yanzu, wanda bai dace ba, kuma babu adalci a cikinsa. Ya ce musamman, tsarin hada-hadar kudi na bukatar gaggarumin sauyi.

Kawo yanzu, sama da kasashe 20 ne suka bayyana bukatar zama sabbin mambobin BRICS a hukumance, cikinsu har da Saudiyya da Iran da hadaddiyar Daular Larabawa da Argentina da Indonesia da Masar da Habasha.

Carlos Correa ya kara da cewa, duk da cewa har yanzu, kungiyoyin G7 da G20 suna da tasiri sosai a harkokin duniya, kungiyoyi ne da manyan kasashe suka mamaye. Amma BRICS na taka muhimmyar rawa wajen tabbatar da daidaito ga karfin G7 da G20. Kana tana lalubo mafitar da ta dace da muradun kasashe masu tasowa.

BRICS kungiya ce ta manyan kasashe masu tasowa da suka hada da Brazil da Rasha da India da Sin da Afrika ta kudu, wadda za ta gudanar da taron shugabanninta na kasashe da gwamnatoci a birnin Johannesburg daga ranar 22 zuwa 24 ga watan nan na Augusta. (Fa’iza Mustapha)