Shin ko lokaci ya yi da bankunan Amurka za su koyi darasi?
2023-08-10 15:08:24 CMG Hausa
Kamfanin Moody's mai bincike game da hada hadar cinikayyar takardun lamuni, wato daya daga manyan kamfanonin kasa da kasa 3, dake auna mizanin yiwuwar biyan bashi, ya sauke kimar wasu kanana, da matsakaitan bankunan Amurka 10, ya kuma sanya karin wasu manyan bankunan kasar 6, ciki har da U.S. Bancorp, a layin wadanda yake nazarin sauke matsayin su. Wannan na faruwa ne a gabar da tuni wasu bankunan kasar 11 ke fama da koma baya.
Bayan bullar wannan labari a ranar Litinin, hannayen jarin wadannan bankuna da kamfanin Moody's ya sauke matsayin su sun fadi warwas, lamarin da ya kuma shafi kimar wasu manyan bankunan kasar.
Cikin ‘yan kwanaki kalilan, manyan cibiyoyin dake auna hadarin karbar lamuni biyu, sun sauke matsayin awon yiwuwar biyan bashin wasu bankunan Amurka, wanda hakan ya faru ne bisa karfafan dalilai.
Manazarta na ganin hakan ya biyo bayan tsawon lokaci ne da Amurka ta shafe, tana dibar lamuni kan kudin kasar wato dala. Hakan ne ya sanya lumunin gwamnatin Amurka, wanda a baya yake da matukar tsaro, a yanzu yake cike da hadurra.
Bugu da kari, yawan nuna yatsa da manyan kamfanonin auna mizanin yiwuwar biyan bashi na kasa da kasa ke yi ga Amurka, ya zamo tamkar wani gargadi ga rashin makama, ta jagorantar harkokin tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.
A matsayinsa na muhimmin bangaren raya tattalin arzikin Amurka, fannin ayyukan banki na cikin rudani, wanda hakan ya haifar da mummunan tasiri ga kasar. Sai dai abun tambaya a nan shi ne, ko jagororin kasar ta Amurka za su koyi darasi? (Saminu Alhassan)