logo

HAUSA

Yadda Amurka ke kwaton albarkatun kasa da kasa da sunan yaki da ta’addanci

2023-08-10 22:27:42 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

 An kara ba da rahoton yadda Amurka ta saci albarkatun Syria. An ce, a farkon wannan watan da muke ciki, sojojin Amurka da ke Syria sun yi jigilar tarin bawon alkama da suka sata daga arewa maso gabashin Syria zuwa sansaninsu da ke arewacin kasar Iraki. Ba a jima ba, sojojin sun kara yin jigilar mai da suka sata daga gonakin mai dake arewa maso gabashin kasar. Kididdigar da aka yi ta shaida cewa, cikin makon da ya gabata ne, sojojin Amurka suka saci mai da yawansa ya kai a kalla daruruwan ton daga Syria.

Hasali ma dai, tun bayan da Amurka ta jibge sojojinta a kasar ta Syria a shekarar 2015 bisa sunan wai “yaki da ta’addanci”, ba ta ko taba daina wawushe albarkatun kasar ba. Har ma don samun saukin aikin, ta girke sojojin kasar musamman a yankunan da aka fi noman hatsi da ma hakar mai a kasar. Alkaluman da gwamnatin Syria ta samar sun shaida cewa, sama da kaso 80% na mai da aka samar a kasar a farkon rabin shekarar 2022, sojojin Amurka ne da ma dakarun da suke wa goyon baya suka sace.

Yanzu haka, kimanin kashi 90% na al’ummar kasar Syria na cikin kangin talauci, kuma kashi 2/3 nasu na dogara ga gudummawar jin kai da aka samar musu, baya ga sama da rabinsu ba su iya samun isassun abinci. Duk da haka, Amurka wadda kullum ke yi wa kanta ikirarin “mai fafutukar kare hakkin dan Adam”, ba ta daina sace albarkatun al’ummar kasar Syria ba, har ma ba ta ko boye laifin da ta aikata ba, ganin yadda tsohon shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya amince a fili cewa, dalilin kasancewar sojojin Amurka a Syria shi ne don kwace mai na kasar. Mataimakiyar shugaban kasar ta Amurka Kamala Harris ma ta bayyana cewa, “cikin dimbin shekarun baya, Amurkawa sun yi ta yin fada ne don albarkatun mai.”

Lallai maganar madam Harris ta tono mana sirrin yakin da kasarta ta tayar da sunan yakar ta’addanci a kasashe da dama, ciki har da Afghanistan da Iraki da Syria da sauransu. Abin da a bakinta ta ce wai “yaki da ta’addanci”, a hakika abu ne da zai taimaka ga bauta wa moriyar kasar ne kawai.

Da zaran Amurka ta ga albarkatun da take so a wata kasa, to, samar da dalili ne kawai ya rage ta yi don kwace su. (Mai Zane: Mustapha Bulama)