logo

HAUSA

An fara tattaunawa wajen bullo da sabbin dabarun gida wajen kare ambaliyar ruwa a jihar Yobe

2023-08-10 09:35:35 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya tare da hadin gwiwa da shirin kare muhalli na kasa da kasa ACRE-SAL sun gudanar da wani taron wayar da kai na yini daya kan sabbin dabarun gida wajen kare tasirin annobar ambaliyar ruwa a jihar.

An dai gudanar da taron ne a garin Damaturu, fadar gwamnatin jihar, inda aka gayyato al’umomi daban daban daga kananan hukumomin jihar 17 domin karawa juna sani a kan rawar da kowa zai taka wajen kare jihar daga fuskantar matsalolin ambaliyar ruwa a bana.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Jihar Yobe tana daya daga cikin jihohin tarayyar Najeriya da suka fuskanci mummunar asarar rayuka da kaddarori sakamakon ambaliyar ruwa na shekara ta 2022, sannan kuma a halin yanzu jihar na cikin jerin jihohin da hukumar hasashen yanayi ta tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za su fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a damunar bana.

Da yake jawabi yayin bude taron, gwamnan jihar ta Yobe Mai Mala Buni wanda kuma ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Baba Malam Wali kira ya yi ga majalissun kananan hukumomin jihar da su dukufa wajen gangamin wayar da kan al’umomin dake yankunansu a kan yadda za su shiryawa duk wata annoba ta ambaliyar ruwa, tare da nuna masu muhimmancin yashe magudanan ruwa.

Dr. Mohammad Goje shi ne babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawan ta jihar Yobe SEMA.

“Wannan taro ba shi ne na farko ba, shi ne na uku mun yi na kananan hukumomi, mun je kauyuka mun wayar da kai, yanzu kuma mun kara tara mutane a wuri guda, makasudin taron shi ne mai girma gwamna ya bukaci a tara mutane a gaya musu matsalolin da ake hasashen samu na ambaliyar ruwa, sannan kuma su gaya mana wane irin dabaru ne suke da shi wanda za su ba mu mu yi amfani da shi domin mu samu sauki, wannan ya biyo bayan wani abu da muka lura da shi a shekarar bara, akwai garuruwan da muka je kai musu dauki na ambaliyar ruwa mun je musu da kayan abinci, amma a wannan lokaci suke gaya mana cewa su ba abinci suke nema ba empty buhu suke nema wanda za su cika su da yashi ko kasa domin su kare garin su”. (Garba Abdullahi Bagwai)