logo

HAUSA

Gasar FISU ta ba da damar hade kan matasa daga mabanbantan yankuna in ji shugaban tawagar Singapore

2023-08-09 22:01:01 CRI

 

An kawo karshen gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa ko FISU a birnin Chengdu na kasar Sin, masu lura da yanayin gasar na ci gaba da bayyana mahangar su, game da tasirin gasar, musamman wajen hada kan matasan sassan duniya daban daban.

A cewar shugaban tawagar daliban kasar Singapore dake halartar gasar, kuma jagoran majalissar kungiyoyin shirya wasannin daliban jami’o’in  kasar Jimmy Ye, gasar ta dinke rukunonin matasa daban daban waje guda.

Jimmy Ye, ya jinjinawa kyakkyawan yanayin sassan jami’ar Chengdu, da kuma yanayi mai kayatarwa na kauyen wasanni da aka tanada domin masu fafatawa a gasar ta bana.

Ya ce "Yayin da muke kewayawa cikin sassan jami’ar a mota, mun ga kayayyakin wasanni da dama da suka burge mu. Akwai abubuwan jin dadin rayuwa, da tsarin gine gine masu ban sha’awa da kayatarwa. Kaza lika, wani bangare mai burgewa shi ne yadda aka yi amfani da fasahohin zamani marasa gurbata muhalli a kauyen na ‘yan wasa. Motar Bas da ta kewaya da mu tana amfani ne da lantarki, na kuma fahimci cewa, wasu daga dakunan dalibai dake cikin jami’ar na amfani ne da lantarki. Bugu da kari, tsarin sarrafa shara na dakin cin abinci dake jami’ar na da ban sha’awa.

Jimmy Ye, yana ganin cewa, shigar da fasahohin zamani cikin harkokin gudanar da wasanni, da harkokin rayuwar yau da kullum na tawagar Singapore abun a yaba ne

Ya ce " Mashirya gasar sun tsara wata manhaja ta wasanni mai kunshe da abubuwa daban daban. Ga misali, idan kana son dabbar panda, kana iya neman shiga tawagar masu zuwa kallonta, ta amfani da manhajar a wayar ka ta salula. Duk da kalubalen zafin rana da ake fama da shi yanzu haka a Chengdu, halayyar mutanen birnin ta karbar baki, da sabo da mutane ta sa mun ji dadin yawo sosai a birnin.

Ya ce "Kowa da kowa, tun daga kan jami’ai har zuwa masu aikin sa kai, sun kasance masu girmama mu, da karbar baki hannu biyu-biyu. A ko ina cikin kauyen wasannin, har a dakin cin abinci suna ta gaishe mu. Sun sa mun ji a ran mu cewa, mun samu karbuwa, kuma muna da martaba"

Ita dai tawagar daliban Singapore na kunshe ne da ‘yan wasa 121, wadanda ke fafata a gasar ta FISU, wadda za a kammala zuwa ranar 8 ga watan nan na Agusta.

Game da hakan, Ye ya ce burin tawagar su shi ne su yi sabo da jama’a daga sassan duniya daban daban, musamman ma al’ummar kasar Sin. Kana su na fatan kara fahimtar al’adun kasar. Ya ce rabon sa da ziyartar birnin Chengdu yau shekaru 14 ke nan, kuma a wannan karo ya ga manyan sauye sauye da birnin ya samu.

Ye ya kara da cewa, "A baya can ma, birnin yana da kayatarwa matuka, amma sam bai kai kayatarwar birnin a yanzu ba. Filin jiragen sama da muka sauka a yanzu sabo ne, kuma kana iya ganin sabbin gine gine na zamani a dukkanin bangarorin hanyar mota."

Jami’in ya kuma tabo batun tasirin wannan gasa ta FISU, wadda ya ce makasudin ta shi ne kulla kawance, ta yadda matasan kasa da kasa za su mayar da hankali ga abubuwan da suka hada su maimakon banbancen dake tsakanin su.

Jimmy Ye ya ce "Burin mu shi ne har kullum mu yada kyawawan dabi’un mu na bai daya a matsayin mu na ‘yan adam; wato dabi’un abota, da kauna, da kyautatawa, da godewa. Ya kamata a karfafa gwiwar matasa daga dukkanin sassan duniya, yadda za su kara azamar fahimtar junan su."  (Saminu Alhassan)