Matakan Kasar Sin na yaki na ambaliyar ruwa domin kokarin kare rayukan fararen hula da dukiyoyinsu
2023-08-09 10:03:26 CMG Hausa
A kwanakin baya ne, yankin Beijing-Tianjin-Hebei da wasu sassan kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama, da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 140 da suka gabata, wanda ya haddasa ambaliya da ma barnar dukiya da rayuka. Bayan faruwar lamarin, mahakuntan kasar Sin sun tura tawagogin aikin ceto daban-daban don gudanar da ayyuka tinkarar wannan bala’i.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da ceto mutanen da suka bace ko kuma suka makale a sanadiyar ambaliyar ruwa da bala'o'in yanayi, a wani umarni da ya bayar kan aikin da ya shafi rigakafin ambaliyar ruwa da agajin bala'o'i.
Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya bukaci a yi kokarin rage yawan asarar rayuka.
Hukumomin gwamnatin kasar Sin sun ware karin yuan miliyan 350 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50 don taimakawa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a biranen Beijing da Tianjin, da lardin Hebei da kuma lardunan arewa maso gabashin kasar Sin.
Hukumomi masu kula da ayyukan dakile ambaliyar ruwa sun bukaci a kara kaimi wajen aikin ceto da ba da agaji a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a yankunan arewa da arewa maso gabashin kasar.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar ta riga ta ware tsabar kudi har yuan miliyan 520 a cikin asusun ba da agajin bala'o'i na kasar ga wadannan yankunan da bala’in ya shafa, a cewar ma'aikatar kudi da ma'aikatar agajin gaggawa. Bugu da kari, wasu sanannun masu mallakar kamfanoni da ‘’yan kasuwa da taurarin fina-finai ma sun bayar da gudummawarsu fiye da RMB yuan biliyan 1 ga aikin dakile bala’un ambaliyar ruwa da suka faru a sassa daban daban na kasar Sin.
Bayanai na nuna cewa, yanzu kusan al’amura sun dawo kamar yadda suke a baya a wadannan wurare. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)