An rufe gasar daliban jami’o’in kasa da kasa karo na 31
2023-08-09 15:05:54 CMG Hausa
An rufe gasar daliban jami’o’in kasa da kasa karo na 31 a jiya 8 ga wata da dare, a birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A cikin kwanaki 12 da suka wuce, dalibai ‘yan wasa 6500 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 113, sun fafata a fannoni 269 na wasanni 18, tare da karya matsayin bajimta sau 22. Baya ga haka, sun kuma karfafa fahimtar juna, da dankon zumunci a tsakaninsu.