logo

HAUSA

Wane ne ya shirya rikicin karamin tsibirin Ren’ai Jiao?

2023-08-09 15:27:46 CMG Hausa

Hukumar ’yan sandan tsaron teku ta kasar Sin, ta fitar da wani hoton bidiyo a jiya, wanda ya nuna jirgin ruwan ’yan sanda tsaron teku na watsa ruwa a matsayin gargadi kan jiragen ruwan Philippines da suka shiga cikin yankin ruwan dake hannun riga da Ren’ai Jiao na tsibiran Nansha na kasar Sin. 

Sai dai Amurka ta shafawa wannan halaltaccen hakki na tabbatar da tsaro bakin fenti.

Karamin tsibirin Ren’ai Jiao wani bangare ne na tsibiran Nansha na kasar Sin. A ranar 9 ga watan Mayun 1999, wani lalataccen jirgin ruwan yaki na rundunar sojin ruwan Philipines ya isa Ren’ai Jiao, inda aka yi ikirarin kasan jirgin na yoyo don haka aka ajiye shi a arewa maso yammacin karamin tsibirin Ren’ai Jiao kuma aka rika tura sojoji suna aikin karba-karba wajen kula da shi. Tun daga wancan lokaci, Philippines ke ta alkawarin dauke wannan jirgin yaki, amma ta gaza cikawa. Sun kuma yi yunkurin gyara shi tare da girke karin sojoji, har ma da mamaye wannan karamin tsibiri na Ren’ai Jiao na dindindin.

A lokaci guda, Amurka ta karfafawa Philippines baya tare da taimaka mata, ta kuma tura jiragen soji da na yaki domin hada gwiwa da taimakawa a tekun. 

Me kake tunanin Amurka za ta yi idan jiragen ruwa na kasashen waje suka shiga yankinta na ruwa ba bisa ka’ida ba? Wadanne irin matakai Amurka za ta dauka a kan jiragen idan suka zauna a yankinta na ruwa?

Batun na tekun kudancin kasar Sin ba shi da alaka da Amurka. Amma a shekarun baya-bayan nan, Washington na ta yada karairayi game da barazanar da ’yancin shiga tekun kudancin kasar Sin ke fuskanta, lamarin dake haifar da tankiya tsakanin kasashen yankin. Batun na Ren’ai Jiao ya kara nuna yadda Amurka ba ta son ganin zaman lafiya a yankin tekun kudancin Sin, da kuma yadda take jiran damar tunzura al’amura a yankin. (Faeza Mustapha)