logo

HAUSA

Wang Yi zai ziyarci Singapore, Malaysia da Cambodia

2023-08-09 19:57:54 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS, zai ziyarci Singapore, Malaysia da Cambodia daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Agusta bisa gayyatar takwarorinsa na kasashen ukun.

Da yake amsa tambayar manema labarai dangane da ziyarar da Wang zai yi da kuma yadda kasar Sin ke kallon dangantakarta da kasashen uku, kakakin ma'aikatar ya ce, dangantakar Sin da Singapore da Malaysia da Cambodia na samun gagarumin ci gaba. (Yahaya)