logo

HAUSA

Tsohon ministan yawon bude ido na Nijar ya kirkiro kungiyar siyasa dake neman a maido da mukamin shugaba Bazum

2023-08-09 19:43:37 CMG Hausa

A jiya 8 ga wata ne tsohon ministan yawon bude ido na jamhuriyar Nijar Rhissa Ag Boula ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce ya kirkiro wata kungiyar siyasa mai suna "Republic Resistance Council" (CRR) da nufin maido da mulkin hambararren shugaba Mohamed Bazum da kama jagoran juyin mulkin wato Abdourahmane Tchiani.

Sanarwar ta ce kungiyar za ta goyi bayan yunkurin kasashen duniya na maido da tsarin mulki ta dimukuradiyya a Nijar. Wannan ita ce kungiya ta farko da ta fito fili domin yakar sojojin da suka kwace mulki tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a ranar 26 ga watan Yuli. (Yahaya)