logo

HAUSA

Sharhi: Rmb Yuan Na Shirin Tumbuke Dalar Amurka

2023-08-07 15:49:38 CMG HAUSA



DAGA YAHAYA

A cikin shekaru 45 da suka gabata, tattalin arzikin ƙasar Sin ya samu bunƙasuwa sosai, inda ya zama na biyu mafi girma a duniya. Ƙasar ita ce mafi girma a duniya wajen fitar da kayayyaki da kasuwanci ga yawancin ƙasashe. Sai dai har yanzu kuɗin ƙasar na RMB Yuan na baya wajen hada-hadar kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Ƙasar Sin ta sake tsallake wani mataki a yunkurinta na rage dogaro da dalar Amurka yayin da amfani da kuɗin Sin RMB Yuan wajen hada-hadar cinikayyar tsakanin ƙasashe a rubu’i na biyu na bana ya zarce kuɗin Amurka a karon farko. Kason kuɗin cikin gida na kuɗaɗen da ƙasar Sin ta biya a tsakanin ƙasashe ya ƙaru da kashi 49 cikin ɗari a karshen watan Yuni daga kusan sifili a shekarar 2010. Kason dalar Amurka ya fadi zuwa kasha 47 cikin ɗari daga kashi 83 cikin ɗari a daidai wannan lokacin. Wannan gagarumar nasarar da aka samu ta nuna yadda ƙasar Sin ke samun bunƙasuwar tattalin arzikinta, da ƙaruwar tasirin kuɗinta.

Musamman ma, RMB Yuan ya tashi daga matsayinsa na 35 a shekara ta 2001, ya zama na biyar mafi yawan kuɗin da aka fi ciniki da shi a duniya. Har ila yau, ya inganta a matsayi kuɗin kashewa a duniya, a halin yanzu yana matsayi na biyar bayan dalar Amurka, Euro, Fam na Birtaniya, da Yen Japan. Wanda ya kasance a matsayi na 30 a shekara ta 2011.

Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun nuna cewa an canza matsayin dala daga hanyar hada-hadar kasuwanci da musayar fasaha zuwa makamin siyasa. Sakamakon haka, ƙasashe da yawa sun zaɓi rage hannun jarinsu a cikin lissafin baitulmalin Amurka, sun zabi sarrafa kadarorinsu ta hanyar haɓaka ajiyar zinariyarsu. Har ila yau, sun zaɓi gudanar da kasuwancinsu tsakanin sauran ƙasahse ta hanyar amfani da kuɗaɗen cikin gida.

 Mu dauki Rasha a misali, ba ta da wani zaɓi illa ta fara amfani da wasu kuɗaɗe wajen cinikin kasa da kasa. Ta fara karɓar kuɗaɗen man fetur, iskar gas, da kwal a yuan, sa’an nan Moscow ta ƙara yawan hannun jarinta na RMB Yuan a asusun ajiyarta na waje. Manyan kamfanonin Rasha, irin su Rosneft, sun ba da lamunin RMB RMB Yuan. A cewar Bloomberg, RMB Yuan yanzu ya zama mafi yawan kuɗin hada-hadar kasuwanci a Rasha.

Bayan da ƙasar Rasha ta fara amfani da kuɗin Yuan sosai, wasu ƙasashe sun fahimci alfanun da ke tattare da hakan, kuma sun ga wata dama ta rage dogaro da dalar Amurka, lamarin da ya haifar da sarkakiya. A farkon wannan shekara, Beijing ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin ƙasashen biyu da Brazil don samar da waken soya. Yarjejeniyar na ba da damar musayar kai tsaye tsakanin Yuan da Real ta Brazil. A watan Afrilu, Argentina ta ba da sanarwar sauya sheka daga amfani da dala zuwa yuan wajen shigo da kayayyaki daga Sin.

Indiya na amfani da kuɗaɗen da ba na dalar Amurka ba, irin su Dirhami na UAE da Ruble na Rasha, don biyan mafi yawan kuɗin man Rasha da suke shigo da su. Hakazalika, Bangladesh ta fara biyan Rasha da yuan kuɗin gina tashar makamashin nukiliya. Iraqi na da niyyar amfani da yuan a matsayin kuɗin biyan kayayyakin da take shigo da su daga Sin. Faransa ta amince da yuan a matsayin biyan kuɗin iskar gas da aka saya daga wani kamfanin mai na ƙasar Sin.

A cikin wani rahoto da aka wallafa a mujallar Time, ministan tattalin arziki da kuɗi na jama'ar Bolivia Marcelo Montenegro ya ce "Mun riga mun fara amfani da yuan. Gaskiya ne kuma kyakkyawan farawa ... masu fitar da ayaba, zinc, da itace, suna gudanar da hada-hadar kuɗi a yuan, da masu shigo da motoci da manyan kayayyaki."

An kuma bayyana cewa, a tsakanin watan Mayu da Yuli na bana, Bolivia ta yi hada-hadar kuɗi da ta kai kuɗin Sin yuan miliyan 278, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 38.7, wanda ya kai kashi 10 cikin 100 na cinikin ƙasashen waje.  Ban da wannan kuma, ƙasar Sin ta zama abokiyar cinikayya ta biyu mafi girma a ƙasar Bolivia, kuma babbar hanyar shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, kuma haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu ta shafi bangarori daban-daban, da suka haɗa da kayayyakin more rayuwa, da harkokin sararin samaniya, da fasahar watsa labaru, da raya mai da iskar gas. Ta kuma yi la'akari da yiwuwar amfani da kuɗin kasar Sin wajen biyan basussukan da asusun lamuni na duniya IMF ke bin ta.

Ana sa ran taron BRICS mai zuwa da za a yi a cikin watan Agustan nan a Afirka ta Kudu, zai tattauna kan aikace-aikace daga ƙasashe masu tasiri da dama da ke neman shiga ƙungiyar. Yanzu an lura cewa mahalarta taron suna shirye don tallafawa gabatar da kuɗi mai zaman kansa a  madadin dalar Amurka. Daga cikin masu neman wannan matsayi har da kuɗin Yuan, tun da yawan GDPn ƙasar Sin ya kai kashi 71 cikin 100 na adadin da ake ciki yanzu. Yayin da takarar tasirin darajar kuɗi ke kankama, bari mu ari kalaman wani babban dan wasan hockey Wayne Gretzky da ya ce, "a maida hankali a inda kwallon zai sauka, ba inda kwallon yake ba." Lallai tasirin kuɗi a hada-hadar kasuwancin duniya ya baro dalar Amurka yayin da yuan na kasar Sin ke shirin tumbuke dalar ta Amurka. (Yahaya)