logo

HAUSA

An kammala taron tattaunawa game da rikicin Ukraine a Jeddah

2023-08-07 10:31:48 CMG Hausa

Wakilan kasashe daban daban mahalarta taron tattaunawa game da rikicin Rasha da Ukraine sun kammala taronsu jiya Lahadi a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, inda suka yi kira ga sassan kasa da kasa da su ci gaba da kwazon zakulo hanyoyin cimma matsaya, domin wanzar da zaman lafiya.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Saudiyya na cewa, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin hawa teburin shawara, matakin da suka ce ya samar da mabanbantan dabaru, da shawarwari, yayin taron wuni 2 da suka kammala a wannan karo.

Taron na wannan lokaci dai ya samu jagorancin ministan cikin gida, kuma mashawarci ta fuskar tsaro ga masarautar Saudiyya Musaad bin Mohammed Al-Aiban. Kazalika ya hallara mashawarta a fannin tsaro, da wakilai daga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 40, ciki har da na Sin da MDD. (Saminu Alhassan)