Aure mai farin ciki yana taimakawa wajen murmurewa daga ciwon zuciya
2023-08-07 11:01:31 CMG Hausa
Wasu nazarce-nazarce sun tabbatar da cewa, aure mai farin ciki yana taimakawa lafiyar jiki da ma tunani. Masu nazari da suka fito daga kasar Amurka sun gudanar da nazarinsu ne kan yiwuwar samun farfadowa daga ciwon zuciya sakamakon aure mai farin ciki. Nazarinsu ya yi na’am da hakan.
Jaridar The Times ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewa, masu nazari daga jami’ar Yale ta kasar Amurka sun yi bincika kan masu fama da ciwon zuciya dubu 1 da dari 5 da 93 wadanda suka kwanta a asibitoci guda dari 1 da 3 a Amurka. Inda suka bukace su da su amsa tambayoyi dangane da yanayin zaman aurensu da lafiyarsu. Matsakaitan shekarun wadannan masu fama da ciwon zuciya sun kai 47 da haihuwa. Shekara guda bayan amsa tambayoyin, masu nazarin sun ci gaba da bincika kan yadda suke murmurewa daga ciwon.
Sakamakon nazarin ya nuna cewa, a cikin wadannan masu fama da ciwon zuciya, matan da yawansu ya kai kaso 40 da mazan da yawansu ya kai kaso 30 sun fuskanci babban matsin lamba daga aurensu. A cikin takardar binciko lafiyar jiki da ma tunani mai maki 12, matsakaicin makin da wadannan mutane suka samu ya yi kasa da 1.6 da 2.6, gwargwadon sauran mutane. Idan an kwatanta su da wadanda ba sa fuskantar matsin lamba da kuma wadanda suke fuskantar dan matsin lamba daga yanayin zaman aurensu, wadannan mutane sun fi yiwuwar fama da ciwon kirji, kana sun fi yiwuwar kwantawa a asibiti sakamakon dalilai da dama.
Jaridar Daily Mail ta Birtaniya ta ruwaito kalaman masu nazarin da cewa, nazarinsu ya nuna cewa, matsin lambar da ake fuskanta a zaman rayuwar yau da kullum, alal misali, ta fuskar aure, za ta yi illa kan yadda baligai suke samun farfadowa daga ciwon zuciya da suke fama da su. Kana kuma masu nazarin suna ganin cewa, babban matsin lamba da ake fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kuma aiki, su ma za su yi illa kan yadda suke warkewa.
Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, kamata ya yi likitoci su binciko matsin lambar da masu fama da ciwo suke fuskanta yayin da suke murmurewa daga ciwon, a kokarin bambanta wadanda ba sa samun saurin murmurewa ko wadanda suka fi yiwuwar sake kwantawa a asibiti, ta haka likitocin za su kara mai da hankali kansu a kan lokaci. (Tasallah Yuan)