logo

HAUSA

Mene ne ainihin Xinjiang? Jakadu daga kasashen waje sun sami amsar

2023-08-07 19:51:51 CMG Hausa

Kwanan nan, jakadan Dominica a kasar Sin, Martin Charles, ya kammala ziyararsa ta farko zuwa yankin Xinjiang. A cikin kwanaki 5, shi da wasu jakadu daga kasashe 24 dake kasar Sin sun ziyarci Kashgar, da Kuche, da Urumqi, inda suka fuskanci al'adun gargajiya da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar yankin Xinjiang kai tsaye.

Masu iya magana kan ce gani ya kori ji. A cikin 'yan shekarun nan, sama da jami'an gwamnati 2000, da malaman addini, da 'yan jarida daga kasashe sama da 100 da kungiyoyin kasa da kasa sun ziyarci yankin Xinjiang, inda suka shaida ci gabanta na tattalin arziki da zamantakewar al’umma. A ra'ayin Kaba Ibrahim Sinkun, wani jami'in diflomasiyyar kasar Guinea dake kasar Sin ya ce, siyasa ce dalilin da ya sa kafofin watsa labaru na yammacin duniya suke yi wa Xinjiang kallon "kufai",   kuma sun yi amfani da wannan damar sun shafa wa kasar Sin bakin fenti. Suna kwatanta kasar Sin ga duniya ta son ran su, kuma ba su damu da mutanen da ke zaune a nan, ko yadda suke rayuwa ba.

A lokaci guda kuma, bayanai sun nuna gaskiya. An kawar da talauci a Xinjiang baki dayanta ya zuwa karshen shekarar 2020. A farkon rabin wannan shekara, yankin Xinjiang ya samu karuwar GDPn da ya kai yuan biliyan 854.208, wanda ya karu da kashi 5.1 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. Daga watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara kuma, yawan masu yawon bude ido da suka ziyarci yankin Xinjiang ya kai miliyan 102, wanda ya karu da kashi 31.49 cikin dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Yahaya)