logo

HAUSA

Ni Xialian: Jarumar basiniya da ke fafatawa a fagen wasan kwallon tebur na duniya

2023-08-07 14:16:13 CMG Hausa


Labarin Ni Xialian, mai shekaru 60 kuma ‘yar wasa ta kungiyar wasanni ta kasar Luxembourg haka kuma ‘yar wasan kwallon tebur mafi shekaru a tarihi, ya karade shafukan sada zumunta na kasar Sin. Wasu masu amfani da kafar intanet sun bayyana cewa, “ Ta kasance abun alfahari ga kasar Sin da Luxemburg.” Ni Xialian, wadda tsohuwar ‘yar wasa ce ta kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin, ta koma Luxembourg ne a shekarar 1991, kuma tun daga shekarar 2000, ta fafata a gasar wasannin Olympics har sau 5.

An haifi Ni Xialian ne a birnin Shanghai a shekarar 1963, kuma ta shiga kungiyar ‘yan wasan kwallon tebur ta Shanghai a shekarar 1978. A shekarar da ta biyo baya kuma, ta shiga kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin.

Yayin gasar zakarun kwallon tebur ta duniya karo na 37 a birnin Tokyo na kasar Japan a 1983, Ni Xialian ta taimakawa kungiyar mata ‘yan wasan kwallon tebur samun lambar yabo, haka kuma ta samu lambar Zinare a wasan da ake hada jinsi biyu, tare da dan tawagarta Guo Yuehua. Baya ga wannan, ta kuma lashe lambar tagulla tare da ‘yar wasa Cao Yanhua, a gasar ‘yan wasa mata da ake hada ‘yan wasa 2. 

Shekaru biyu bayan nan, Ni Xialian da Cao Yanhua suka kara lashe lambar Azurfa a gasar ‘yan wasa mata, yayin gasar zakarun kwallon tebur ta duniya karo na 38 a Goteborg na kasar Sweden.

Ni Xialian ta yi ritaya daga kungiyar kasar Sin ne a shekarar 1986, daga nan ta koma kasar Jamus a 1989. Shekaru biyu bayan nan kuma ta koma Luxembourg. Sai dai kaunar da take yi wa wasan kwallon tebur bai bar ta ta yi ritaya ba. Sai kuma ta tsunduma a fagen fafatawa, ta kuma lashe gasarta ta farko a 1998.

Duk da shekarunta, Ni Xialian ita ce babbar ‘yar wasan kwallon tebur a Luxembourg, kuma ta jagoranci kungiyarta ta Luxembourg zuwa gasannin zakarun nahiyar Turai da dama.

Ni Xialian ta ce, “ina buga wasan kwallon tebur irin na gargajiya na kasar Sin, wato rike filafili kamar yadda ake rike biro, kuma ina sanya roba a jiki, wanda ke da dan fa’ida kadan, musamman saboda shekaruna sun ja. Salona ba ya bukatar karfi da yawa ko guje-guje, kuma yana ba ni damar yin wasa cikin basira.” Ta kara da cewa, sirrin nasarorinta shi ne daddadiyar kaunarta ga wasa kwallon tebur da kuma yadda take amfani da hikima a wasan. 

A shekarar 2021, Ni Xialian ta kara samun lambar yabo a gasar zakarun kwallon tebur ta duniya a karo na 5. An hada ta wasa da Sarah de Nutte, inda suka lashe lambar Tagulla a gasar rukunin mata a Houston na Amurka.

Da take magana game da shekarunta, Ni Xialian ta ce, “ Yanzu, farin ciki shi ne mafi muhimmanci idan na halarci gasa. Ina jin dadin fafatawa a gasanni daban-daban a wurare mabambanta na duniya. Gwiwata ba ta sanyi muddin na yi iyakar kokarina. Amma dai idan zan samu lambar yabo, to zan yi matukar farin ciki. Amma a kalla ina son in kasance cikin kuzari da shirin fafatawa domin nunawa duniya yadda kwallon tebur ke da kyau.” 

Ni Xialian ta kasance mai matukar kaunar kasarta. Ta ce, “ An haife ni a kasar Sin, kuma na samu horo a Shanghai, wanda ya ba ni damar kwarewa da kara basira. Abu ne mai muhimmanci da daraja a gare ni. Ina matukar godiya ga kasata. Idan babu kasar Sin, ba zan cimma nasarar da na samu ba… abun alfahari ne kasancewa a dandalin duniya, ina nuna basirar Sinawa.”

Ana daukarta a matsayin ‘yar wasa mai daraja ta Luxembourg. “Ana kaunata da bukatata a Luxembourg, kuma ina ganin daya ne daga cikin dalilan da ke sa ni kara fafatawa a fagen gasar kwallon tebur na duniya. Kungiyarmu na da hadin kai. Ina kaunar abotar dake tsakaninmu mambobin kungiyar, kuma ina jin dadin buga wasan kwallon tebur da su,” cewar Ni Xialian. 

Tun daga shekarar 2000, Ni Xialian ta fafata a gasar wasannin Olympics har sau 5. Ta ce, “Na yi ritaya daga kungiyar kasar Sin a shekarar 1986. Ban bugawa kasata wasa a yayin gasar Olympics ba, saboda sai a shekarar 1988 kwallon tebur ya shiga jerin wasannin Olympics.”

A shekarar 1996, Ni Xialian ta ki amincewa da gayyatar Luxembourg ta buga mata wasan Olympics na lokacin zafi a Atlanta ta kasar Amurka. Amma bayan wasu shekaru, Ni ta sauya tunani. Tana ganin cewa, “Abun alfahari ne fafatawa a gasar wasanni mafi girma a duniya.”

Ta halarci gasar wasannin Olympics na Sydney a shekarar 2000 a matsayin ‘yar wasan Luxembourg, ta kuma bude sabon shafin wasa tana mai shekaru 37. Kuma shi ne karon farko da kungiyar Luxembourg ta buga wasa a yayin Olympics. Tun daga lokacin, Ni Xialian ta bugawa Luxembourg wasa yayin wasannin Olympics har sau 4, a Beijing da London da Rio de Janeiro da kuma Tokyo.

Ta kai zagaye na 3 a wasannin Olympics na 2008, sai kuma ta yi rashin nasara a zagaye na biyu na wasannin Olympics na 2012 a London. Yayin bikin rufe wasannin Olympics na Rio a shekarar 2016, Ni Xialian ce ta dauki tutar tawagar kasar Luxembourg. Haka kuma ita ce ‘yar wasa mafi yawan shekaru a wasannin Tokyo na 2022.

A cewar Ni Xialian, ‘yan wasan da suka fafata a wasannin Olympics na nuna kwarin gwiwa a gaban ‘yan kallo. “Ruhin wasannin Olympics na bukatar fahimtar juna da ruhin abota da hadin gwiwa da adalci. Yayin wasannin Olympics, ba mu da bambanci da juna, ba a la’akari da yanayinmu ko inda muka fito ko wasannin da muke bugawa,” cewar Ni Xialian.

Da aka yi mata tambaya game da gasar wasannin Olympics ta Paris ta 2024, Ni Xialian ta ce za ta yi kokari tukuru ta yadda za ta zama gasar wasannin Olympics ta 6 da za ta halarta. Tana da kankan da kai, kuma ta san iyakar juriyar jikinta. Ni Xialian ta ce, “lokaci da igiyar ruwa ba sa jiran kowa. Ba zai yiwu in yi wasa kamar lokacin da nake kuruciya ba. Amma, abu mafi muhimmanci shi ne, kaucewa jin rauni ko rashin lafiya, kuma in ci gaba da kara kokari. Ina zuwa wajen motsa jiki domin kara karfin jiki da lafiya. Cin nasara kan abokan karawa ta hanyar amfani da hakima babban kalubale ne amma mai ma’ana a gare ni.”

Ta kara da cewa, “iyalina, da kungiyata ta ‘yan wasan kwallon tebur da mutanen Luxembourg, suna ba ni goyon baya sosai. Kuma ina da magoya baya. Haka kuma ina alfahari da magoya baya Sinawa. Abun karfafa gwiwa ne a gare ni, kuma hanya mafi dacewa ta saka musu ita ce, yin iyakar kokarina.”

Mijin Ni Xialian wato Tommy Danielsson, shi ne mai horar da ita. A lokacin da Ni Xialian ta hadu da shi a shekarar 1991, shi ne ke horar da kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Luxembourg. “Ban taba jin kadaici ba, domin yana kasancewa tare da ni yayin gasanni daban daban,” cewar Ni Xialian.

“Ba goyon baya a fannin sana’a da shawara kadai mijina ke ba ni ba, yana kuma kulawa sosai da harkokin iyali da taka muhimmiyar rawa a babban iyalinmu. Ina jinjinawa kauna da goyon bayan da yake ba ni, da yadda yake da fahimta. Ina jin cewa, ba ni da damuwa domin yana ba ni tsaro,” cewarta. 

Ba Danielsson ne kadai ke ba Ni Xialian kwarin gwiwa a fannin sana’arta ba, har da danta, wanda likitan mai taimakawa ‘yan wasan motsa jiki ne, kuma ya kan ba ta kulawa bisa kwarewa a duk lokacin da take bukata. 

Ni Xialian ta furta cewa, “ina da babban iyali mai cike da kauna da samar da goyon baya, wanda shi ne babban ginshikin iyalina. Kyakkyawar alakar dake tsakanin iyalina, abu ne mai daraja a gare ni. Kwallon tebur wani bangare ne na rayuwata. Ni ba ‘yar wasa ce kadai ba, ni matar wani ce, kuma uwa kana mai babban iyali, kuma ‘yar kasuwa. Iyalina su ne gaba da sana’ata ta kwallon tebur, domin na yi imanin cewa, iyali mai cike da farin ciki, shi ne tubalin sana’a mai kyau.”

Ni Xialian tana ganin cewa, duk da cewa ba ta wakiltar kasar Sin yanzu, amma wakiltar Luxembourg ma na da ma’ana, ganin yadda take kokarin kulla abota a tsakanin kasashen biyu. 

Ni Xialian ta ce, “a yayin gasannin kwallon tebur, ina wakiltar Luxembourg, a cikin kasar Luxembourg kuma, ina wakiltar Sinawa. A ganina, wannan abu ne mai ma’ana sosai.” (Kande Gao)