logo

HAUSA

Faransa na goyon bayan kokarin da ECOWAS ke yi kan shiga tsakanin rikicin Nijar

2023-08-06 15:40:11 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta fitar da wata sanarwa jiya, inda aka bayyana cewa, ministar wajen kasar Catherine Colonna ta yi tsokaci yayin da take ganawa da Ouhoumoudou Mahamadou, firayin ministan kasar Nijar wanda ke yin ziyara a birnin Paris, fadar mulkin kasar Faransa cewa, kasarta tana goyon bayan kokarin da kungiyar ECOWAS ke yi domin dakile yunkurin juyin mulki a Nijar, kuma ta yi kira da a maido da odar kundin tsarin mulkin kasar nan take ba tare da bata lokaci ba.

Firayin ministan Nijar Mahamadou yana halartar taron kasa da kasa a Turai a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata wato lokacin da aka yi juyin mulki a Nijar, har yanzu bai koma kasarsa ba tukuna.

Yayin ganawar ta su, minista Colonna ta sake jaddada cewa, Faransa tana goyon bayan shugaban Nijar Mohamed Bazoum da sojojin da suka yi juyin mulki suka tsare, da gwamnatin dake karkashin jagorancinsa.

Nijar, muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ta Faransa a bangaren yaki da ta’addanci dake yankin Sahel, a halin yanzu, adadin sojojin Faransa dake Nijar ya kai kusan 1500.

A jiya Asabar, Colonna ta gaya wa kafafen watsa labarai na Faransa cewa, duk da cewa Faransa ba za ta janye sojojinta daga Nijar ba, amma an riga an daina yin hadin gwiwar aikin soja dake tsakanin kasashen biyu sakamakon tasirin juyin mulki.

Rahotanni sun nuna cewa, shugabannin kungiyar ECOWAS sun kira taro cikin gaggawa a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Najeriya a ranar 30 ga watan Yuli, inda suka bukaci sojojin da suka yi juyin mulki da su saki Bazoum tare da maido da mulkinsa nan da nan, idan ba su biya bukatunsu a cikin mako guda ba, ECOWAS za ta dauki daukacin datattun matakai. Amma ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta musunta za ta dauki matakin soja kan Nijar. (Jamila)