logo

HAUSA

Firaministan Nijar ya ce har yanzu yana fatan warware rikicin Nijar ta hanyar diflomasiyya

2023-08-06 19:31:30 CMG Hausa

A wata hira da ya yi da manema labarai a birnin Paris na kasar Faransa jiya, firaministan kasar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya ce har yanzu yana fatan warware rikicin Nijar ta hanyar tattaunawa ta diflomasiyya.

A ranar 26 ga Yuli ne sojoji suka yi juyin mulki a Nijar. A daidai lokacin da Ouhoumoudou Mahamadou yake halartar wani taron kasa da kasa a Turai, kuma yana makale a kasar waje har zuwa yanzu. (Yahaya)