logo

HAUSA

Duniyarmu na da girman da ya ishi kasa da kasa su samu ci gaba tare

2023-08-06 14:24:36 CMG Hausa

Akwai wata kasar da ta kafa sansanonin soja kimanin 750 a ketare, wadanda suka barbazu a kasashe da shiyyoyi 80 na Asiya da Turai da gabas ta tsakiya da Afirka da Latin Amurka, matakin da ya sa ta zama kasar da ta fi yawan mallakar sansanonin soja a duniya.

To, haka ne, ita ce Amurka.

Duk da haka, kasar ta Amurka ta yi ta yada jita-jita cewa wai “akwai barazana daga tashoshin jiragen ruwa da kasar Sin ta zuba jarin gina su a fadin duniya”, wadda ta shelanta cewa wai “tashoshin na iya samar da tallafi ga sojojin ruwan kasar Sin”. Wani abokina dan Nijeriya ya tambaye ni ra’ayina kan batun bayan da ya karanta rahoton.

Lallai furucin ya ba ni dariya, mun sha jin “tarkon bashi” da “sabon salon mulkin mallaka” daga bakinsu a baya... ga shi yanzu har an alakanta tashoshin ruwa wajen shafa wa kasar Sin bakin fenti. Gaskiya sun yi iyakacin kokari wajen dakile kasar Sin.

Sinawa kan ce, ba a damuwa da rashin dalili idan ana son dora laifi kan wani, kuma wannan magana ta dace ayi amfani da ita a kan kasar Amurka, domin kuwa, Amurka ba ta taba mai da hankali a kan abubuwan da kasar Sin ta yi, a maimakon haka, kullum hankalinta na kan ta yaya za ta gano abin da zai shafa wa kasar Sin kashin kaza.

Sanin kowa ne sufurin teku ya kasance hanyar sufuri mafi muhimmanci a hada-hadar cinikin duniya, don haka ma, tashoshin jiragen ruwa na taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasa. Bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, kamfanonin kasar Sin sun yi ta kokarin sa hannu cikin ayyukan gina tashoshin jiragen ruwa a kasashen da suka amince da shawarar, matakin da ya yi matukar inganta samar da guraben aikin yi da ababen more rayuwa da kuma tattalin arzikin kasashen. Misali a Nijeriya, tashar jiragen ruwa ta Lekki da kamfanin kasar Sin ya sa hannun zuba jari da ma gina ta, ta kasance tasha mai zurfin ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, haka kuma daya ne daga cikin jiragen ruwa mafi girma a shiyyar yammacin Afirka. Tun bayan da aka fara aiki da ita a farkon wannan shekara, tashar ta taimaka wajen fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa ketare, musamman ma amfanin gona, an kuma yi hasashen tashar za ta samar da guraben aikin yi kimanin dubu 200 nan da shekaru masu zuwa, wadda za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ga shi irin wadannan tashoshin sun zamanto barazana a bakin kasar Amurka. A hakika, da yardar kasashen ne kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kuma ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidansu ba, balle ma a ce ta haifar da barazana ga tsaron wata kasa. Bisa kididdigar da bankin duniya ya yi, daga shekarar 2015 zuwa ta 2030, kimanin mutane miliyan 40 ne za su fita daga kangin talauci sakamakon hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya.

Don haka ma, akasarin kasashe sun nuna yabo ga hadin gwiwar da suke yi da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya, akasin yadda Amurka da wasu kasashen yamma suka nuna “damuwa”. Dalilin hakan kuma shi ne hadin gwiwar ya karfafa mu’amalar tattalin arziki da al’adu a tsakanin kasashen, tare da kara karfinsu a duniya, matakin da kuma ya ba Amurka matukar damuwa, sakamakon yadda hakan ya zama barazana ga babakeren da ta kafa a duniya. Don haka, sai aka ga Amurka ta na ta kokarin yada jita jita a duniya, a kokarin bata sunan kasar Sin da ma hadin gwiwarta da kasashen duniya.

Sinawa kuma kan ce, “Sai wanda ya sa takalma ne zai san ko ya dace”. Kasashen da suke yin hadin gwiwa da kasar Sin suna da hikima da kuma kwarewa wajen tabbatar da ko hadin gwiwa ya dace ko a’a, kuma ba su bukatar “malami” ya yi musu lacca.

Duk ci gaban da za ta samu, ba za ta kafa babakere ko fadada ikonta a duniya ba, wannan alkawari ne da kasar Sin ta dauka. Amma Amurka a nata bangare, me ya sa ta kafa tarin sansanonin soja a sauran kasashen duniya?

Daga karshe, zan so in ce, duniyarmu na da girman da ya ishi kasa da kasa, ciki har da Sin da Amurka su samu ci gaba tare, ba sai an ci nasara daga faduwar wani bangare ba. Kuma ya kamata a bari kasa da kasa su zabi hanyar ci gaba da suka ga ta dace.(Lubabatu Lei)