Trump ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa kan yunkurin sauya sakamakon zaben shekarar 2020
2023-08-04 09:28:00 CMG Hausa
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya ki amsa tuhumar da gwamnatin tarayya ta yi masa na yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2020.
Da yammacin jiya ne dai aka gurfanar da Trump a gaban wata kotun tarayya da ke Washington,D.C, kwanaki biyu bayan da aka tuhume shi da aikata laifuffuka a hukumance.
Trump ya bayyana a gaban alkalin kotun majistare, don fuskantar tuhume-tuhumen da ake zarginsa da aikata. Sai dai a lokacin da aka nemi jin da bakinsa kan laifuka 4 da ake tuhumarsa da aikatawa, Trump ya amsa cewa, "Bai aikata ba”
A ranar Talatar da ta gabata ce, wani babban alkalin kotun tarayya, ya tuhumi Trump da aikata laifuffuka guda 4, wadanda suka hada da hada baki don damfarar Amurka, da hada baki don hana gudanar da aiki a hukumance, da kawo cikas da yunkurin hana wani aiki a hukumance, da kuma hada baki don tauye hakki. (Ibrahim)