logo

HAUSA

Rasha ta gabatar da hadaddiyar sanarwa ta shugaban kasar da shugabannin kasashen Afirka

2023-08-04 21:11:26 CMG Hausa

A yau ne fadar mulkin kasar Rasha wato Kremlin ta gabatar da hadaddiyar sanarwa ta shugaban kasar Vladimir Putin da shugabannin kasashen Afirka, bayan shawarwarin da suka yi a birnin Saint Petersburg.

Sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 28 ga watan Yuli, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugabannin kasashen Afirka 7 wadanda suka gabatar da kiran shimfida zaman lafiya, sun ci gaba da yin shawarwari a Saint Petersburg game da kiran shimfida zaman lafiyar da aka gabatar a ranar 17 ga watan Yuni.

Shugabannin kasashen da suka halarci shawarwarin sun yi nuni da cewa, an samu babban ci gaba kan daidaita batun jin kai, kuma suna sa ran samun sakamako a nan gaba a wannan fanni. Kana sun yi kira da daukar matakai don kawar da cikas game da fitar da hatsi da takin zamani daga Rasha, inda suka ce ta hakan za a mayar da aiwatar da yarjejeniyar jigilar kayayyakin gona a mashigin tekun Black Sea.(Zainab)