logo

HAUSA

Al’ummun Japan sun sake gudanar da zanga zangar kin amincewa da zubar da ruwan dagwalon nukiliya a teku

2023-08-03 10:56:03 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Japan na ci gaba da yin watsi da ra’ayoyin al’ummun kasa da kasa, da ma Japanawa dake adawa da zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima cikin teku.

Yayin da wa’adin zubar da ruwan ke kara karatowa, karin Japanawa na ci gaba da gudanar da zanga zangar kin amincewa da matakin, ta hanyar gudanar da gangami da sauran wasu karin matakai.

Da yammacin jiya Laraba ma, wasu dandazon Japanawa sun sake yin tururuwa zuwa bakin helkwatar kamfanin samar da lantarki na birnin Tokyo, inda suka yi Allah wadai da shirin kasar na zubar da dagwalon ruwan mai hadari cikin teku, tare da kira ga gwamnatin Japan, da kamfanin lantarkin na Tokyo, da su dakatar da aiwatar da wannan mataki mai hadarin gaske, su kuma sauke nauyin dake wuyan su yadda ya kamata.

Game da ikirarin gwamnatin Japan da kamfanin lantarkin na Tokyo, cewa wai an riga an tace ruwan dagwalon nukiliyar, masu zanga zangar sun ce da zarar an juye wannan ruwan dagwalo cikin teku, tasirin sa zai haifar da mummunar illa ga lafiyar al’umma, da ma zuri’o’in dake tafe. (Saminu Alhassan)