logo

HAUSA

Shugaban Brzail: BRICS za ta iya taka muhimmiyar rawa a duniya

2023-08-03 15:07:13 CMG Hausa

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana cewa, kungiyar BRICS za ta iya taka rawa ta musamman a fadin duniya, domin za ta iya taimakawa wajen rage rashin daidaito ta hanyar baiwa kasashe masu tasowa tallafin kudade ba tare da wasu sharudda masu sarkakiya ba.

Shugaba Lula ya bayyana yayin wata liyafar karin kumullo da manema labarai na kasashen waje cewa, yana da kyakkyawan fata ga taron BRICS karo na 15 da za a yi a Afirka ta Kudu a karshen wannan wata. Yana mai cewa yana da matukar muhimmanci kasashe irinsu Saudiya, da Argentina da sauran manyan kasashen duniya, da ma raguwar kasashe masu tasowa su shiga wannan kungiya. (Ibrahim Yaya)