logo

HAUSA

Bai dace a mayar da wata saniyar ware ba

2023-08-02 09:47:44 CMG Hausa

Kwanan nan, Jamus ta wallafa wata takarda, a karon farko a tarihinta, mai taken "cikakkiyar dabarun ƙasar Sin," manufar rage dogaron tattalin arzikinta da Beijing. Tana mai nuna buƙatar gaggauta "yin taka-tsantsan da haɗarin mu’amala" da ƙasar Sin. Wannan takarda tana yiwa ƙasar Sin laƙabi da "abokiyar harka, da fafatawa, kuma abokiyar adawa a dabarance."

A cikin saƙonsa na martani ga wannan takarda mai shafuka 64 da ya wallafa a shafinsa na tiwita, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce, "Manufarmu ba ita ce a yanke alaƙa da Sin ba. Amma muna son rage dogaro da ita a nan gaba." Yayin da manufar “de-risking” wato "yin taka-tsantsan da haɗarin mu’amala" da ƙasar Sin na iya zama kamar abin sha'awa ga wasu, amma ya zama wajibi a yi la'akari da yadda za a tinkari lamarin ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki, da yiwuwar "abin da zai biyo bayan haka" da kuma "haɗarin yanke hulɗa" da ƙasar Sin wanda bai kamata a yi watsi da su ba”.

Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Jamus a cikin shekaru bakwai da suka gabata, lamarin da ya sa su zama masu taka muhimmiyar rawa wajen cin gajiyar tattalin arzikin juna. Hatta wannan takardar “dabaru” da aka wallafa ba tare da zurfafa tunani ba, ta yarda da cewa, ƙasar Sin ita ce babbar abokiyar ciniki daya tilo ta Jamus. A cewar ofishin ƙididdiga na Tarayyar Jamus, cinikayya tsakaninsu ta zarce dala biliyan 335.3 a shekarar 2022. Kusan kamfanoni 6,000 na Jamus ne ke gudanar da harkokin kasuwanci a ƙasar Sin wanda ake sa ran zai ƙaru.

Ban da haka kuma, binciken da ƙungiyar ’yan kasuwa ta Jamus ta gudanar ya nuna cewa, kashi 77 cikin 100 na kamfanonin Jamus na da shirin faɗaɗa harkokinsu a ƙasar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa. Wadannan bayanai na nuni da muhimmancin dangantakar tattalin arziki tsakanin Beijing da Berlin, wadda za ta fuskanci halin kaka-nika-yi saboda wannan gurguwar tunani.

A matsayinta na ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, ƙasar Sin tana da muhimmin matsayi kuma mai ɗorewa a cikin mizanin samar da kayayyaki a duniya. Kamfanonin Jamus da yawa sun kafa masana'antu a ƙasar Sin kuma sun dogara ga masu samar da kayayyaki na ƙasar Sin don tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki.

Shawarar da Berlin ta yanke na karkata hajojinta daga Sin za ta kasance mai sarƙaƙƙiya, tsada, kuma mai ɗaukar lokaci. Haka kuma, shawarar kau da kai daga ƙasar Sin, za ta kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, wanda zai haifar da ƙaruwar farashin kayayyaki ga masu zuba jari na Jamus, kuma duk wani kokari na mayar da wata kasa saniyar ware, ba zai haifar da da mai ido ga duniya baki daya ba. (Yahaya, Ibrahim /Sanusi Chen)