logo

HAUSA

Fitch ta rage matakin bashin Amurka

2023-08-02 11:03:18 CMG Hausa

Hukumar kasa da kasa dake daidaita kimar kasa, Fitch, ta sanar a jiya Talata cewa, za ta rage matakin bashin da ake bin kasar Amurka daga “AAA” zuwa “AA+”.

Fitch ta ce, ana hasashen yanayin harkokin kudin Amurka zai ci gaba da tabarbarewa nan da shekaru uku masu zuwa, saboda bashi mai yawa da gwamnatin Amurka take ci yana karuwa. Ban da wannan, a cikin shekaru 20 da suka gabata, karfin tafiyar da mulkin Amurka ya ragu, lamarin dake nuna ci gaba da takun saka kan yawan bashin da kasar za ta iya karba gami da kudurori na kurarren lokaci da ake dauka.(Safiyah Ma)