logo

HAUSA

Kaska Za ta Mutu Da Haushin Kifi

2023-08-02 18:45:14 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma yankin Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin wanda ba za a iya taba raba shi daga kasar Sin ba. Kuma, gwamnatin Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar Sin bisa doka. Wannan shi ne muhimmin bayani game da manufar “Kasar Sin daya tak a duniya”, wanda ya samu amincewar gamayyar kasa da kasa.

Duk da cewa kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da kasashen biyu suka aminta da su a kan alakar dake tsakaninsu, amma a wasu lokuta ta kan yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na huldar dake tsakaninta da kasar Sin, inda take ci gaba da hulda da yankin Taiwan na kasar Sin a hukumance, har da neman sanya ta cikin tsarin hukumomin MDD, kamar babban taron majalisar kiwon lafiya ta duniya.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Duk wani kokari na neman jirkita gaskiya, ko kadan ba zai taba yin nasara ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ne.

Haramtaccen matakin Amurka na baya-bayan nan shi ne labarin da shafin intanet na Fadar White House na kasar Amurka ya walllafa cewa, gwamnatin Amurka za ta taimakawa yankin Taiwan na kasar Sin da makamai da horo a fannin soja wadda darajarta ta kai Amurka miliyan 345. Shi ne karo na farko da gwamnatin Biden ta samar da taimakon soja ga yankin Taiwan ta hanyar amfani da “ikon shugaba”.

Wannan mataki na Amurka ya saba yarjejeniyoyin kasa da kasa, kuma tsoma baki ne karara a harkokin cikin gidan kasar, wanda zai kawo illa matuka ga ikon mulki da tsaron kasar Sin, da ma kawo barazana mai tsanani ga zaman lafiya dake kasancewa tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan. Hali aka ce zaren Dutse.

Kamar yadda ruwa da wuta ba za su hadu wuri daya ba, haka ma burin ballewar yankin Taiwan, ya saba da burin wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin na Taiwan. Kuma domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, ya zama wajibi a tabbatar da rashin amincewa da duk wani mataki na ingiza burin “samun ’yancin kan Taiwan". Burin Amurka da ’yan kanzaginta na neman tayar da husuma a yankin Taiwan, ba zai taba yin nasara ba. Haka kaska za ta mutu da haushin kifi. (Ibrahim Yaya)