logo

HAUSA

Bashir Abdullahi: Ilmin da na samu a kasar Sin zai taimake ni wajen gudanar da harkokin kasuwanci

2023-08-01 15:02:36 CMG Hausa

Bashir Abdullahi, dan asalin jihar Kanon tarayyar Najeriya ne, wanda ya gama karatun digiri na farko a kasar Sin kwanan baya. Kana a watan Satumbar bana, zai ci gaba da karatun digiri na biyu a wata jami’a dake birnin Changsha na lardin Hunan.

A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Bashir, ya bayyana abubuwa da dama da suka burge shi a Sin, da fahimtar sa kan ci gaban kasar, gami da bambancin yanayin karatu dake akwai tsakanin gida Najeriya da Sin.

A karshe, malam Bashir ya bayyana kyakkyawan fata, da shawarar sa ga matasan Najeriya. (Murtala Zhang)