logo

HAUSA

Faransa za ta kwashe ‘yan kasarta daga Niger nan ba da dadewa ba

2023-08-01 19:35:47 CMG Hausa

 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta sanar a yau cewa, za a kwashe Faransawa dake Niger nan ba da dadewa ba, kwanaki bayan juyin mulkin shugaba Mohamed Bazoum da kwace ikon kasar ta yammacin Afrika.

A cewar ma’aikatar, ana shirya yadda za a kwashe mutanen. Kuma za a kwashe su nan ba da jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)