Kasashen duniya na bukatar kasar Sin fiye da yadda take bukatarsu
2023-08-01 20:49:46 CMG Hausa
Tun daga karshen makon da ya gabata, ministan harkokin kudin kasar Faransa Bruno Le Maire, ya fara ziyara a kasar Sin, a wani yunkuri na karfafa hadin gwiwa da tattaunawa batutuwan cinikayya da tattalin arziki da kasar Sin. Wannan ziyara dai manuniya ce cewa, Faransa ta san abun da ya dace da ci gabanta da ma na duniya, haka kuma ba ta biyewa ra’ayin sauran kasashen yamma dake gani ko daukar kasar Sin a matsayin barazana, tare da kiraye-kirayen raba gari da ita ba.
A baya-bayan nan, an ga yadda jami’an Amurka, wadda ita ce ke yada jita-jitar “barazanar kasar Sin” da batun “raba gari da kasar Sin”, suka yi ta kai-komo a kasar Sin, shin idan da gaske suna son raba gari da kasar Sin, me ke kawo su? Sanin kowa ne suna zuwa ne da zummar kyautata alakar dake tsakaninsu da ita, musamman ganin yadda Amurkar ke fama da matsalar tattalin arziki. Kamar yadda sakatariyar baitulmalin Amurkar Janet Yellen ta bayyana, raba gari tsakanin tattalin arzikin Sin da Amurka, ba zai taba yiwu ba. A ganina, wani abu ne kawai da Amurka ke furtawa domin yaudarar duniya saboda wasu muradu nata, amma zancen ba haka yake ba a hakikanin gaskiya.
Tabbas, dogaro da kai da neman ci gaba bisa yanayin kasa, abu ne da Sin ke kira da bada kwarin gwiwar aiwatarwa ga kasashen duniya, domin ta kasance abar misali a wannan bangare. Amma kiraye-kirayen raba gari da Sin ko mayar da ita saniyar ware, abu ne da ba zai amfani kasashen ba har ma da duniya baki daya. Babu wata kasa da za ta bugi kirji ta ce za ta dogara da kanta kadai, ba tare da hada hannu da sauran kasashe ba.
Kuma zuwa yanzu, ya kamata wadancan kasashe masu yada jita-jita su fahimci cewa, suna matukar bukatar kasar Sin fiye da yadda take bukatarsu, kasancewar kasuwarta mai girma, da tubalin tattalin arziki mai kwari da fasahohin zamani da ta mallaka da dimbin kyawawan manufofi da a kullum take samarwa domin jan hankalin ’yan kasuwa da ma kyautata musu yanayin kasuwanci a kasar.
Abun da suka kasa fahimta shi ne, janyewa daga kasar Sin wani yunkuri ne na durkusar da kamfanoninsu da ’yan kasuwa. Kowa ya shaida yadda aka samu tsaikon samar da kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki har ma da hauhawar farashin kayayyaki a lokacin da annobar COVID-19 ta afkawa kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, ba shakka kasashen duniya na bukatar kasar Sin, fiye da yadda take bukatarsu.
Har kullum kasar Sin na ci gaba da fadada bude kofarta da maraba da kamfanoni da ’yan kasuwar kasashen waje, domin samun moriyar bai daya da hada gwiwa domin gina al’umma mai makoma ta bai daya. Wadanda kuma suke ganin nisanta kansu da kasar Sin shi ne mafita a gare su, su yi kuka da kansu idan lamura suka kara tabarbare musu. (Fa’iza Mustapha)