Bayanin Da Amurka Ta Yi Kan Kudurin MDD Yaudara Ce Da Ta YI Wa Al’umma
2023-07-31 22:09:24 CMG HAUSA
Kwanan baya, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da shirin doka dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, inda ta yi shelar cewa, kudurin MDD mai lamba 2758 ya yi na’am da wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD, amma bai shafi wakilcin Taiwan a MDD ba, kuma bai bayyana matsayi kan hulda tsakanin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da Taiwan ba. Matakin ya gurgunta kudurin MDD, kuma Amurka ta yaudari al’umma dangane da batun Taiwan.
Manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ra’ayi daya ne da kasashen duniya suka cimma. Yanzu kasashe 182 ciki had da Amurka, sun kafa huldar jakadanci da kasar Sin bisa manufar. Sun kuma yi alkawarin yin mu’amala da Taiwan ta fuskar al’umma, tattalin arziki da al’adu ba tare da daukar Taiwan a matsayin wata kasa ba.
Kana kuma a cikin wasu muhimman kungiyoyin kasa da kasa, kamar WTO, IOC, APEC da babban taron WHO, a kan tambayi ra’ayin kasar Sin da kuma tattaunawa da Sin dangane da ko a bar Taiwan shiga ciki, da matsayin Taiwan da dai sauransu. Amurka ta gurgunta manufar “kasar Sin daya tak a duniya” bisa dokarta, a yunkurin illata tsari da odar kasa da kasa bayan babban yakin duniya na biyu, da ra’ayi daya da kasashen duniya suka cimma da dokokin kasa da kasa, da manyan ka’idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, lamarin da ya sake shaida cewa, Amurka ta fi illata tsari da odar kasa da kasa.
Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin, kuma Amurka bata da iznin yin bayani kan kudurin MDD mai lamba 2758. (Tasallah Yuan)