logo

HAUSA

Chen Wanghui: Sarauniyar furen Rose dake jagorantar mazauna kauyensu wajen samun wadata

2023-07-31 14:40:17 CMG Hausa


Chen Wanghui, ita ce sakatariyar reshen JKS a kauyen Maoshui na gundumar Xiaojin na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Cikin shekaru 10 da suka gabata, ta jagoranci mazauna kauyen wajen yaki da talauci ta hanyar noman furannin Rose, lamarin da ya kai su ga sauya gundumar Xiaojin zuwa sansanin noman Rose mafi inganci da girma a fadin kasar Sin. Chen ta dukufa wajen hada raya kasuwancin Rose da aiwatar da aikin farfado da kauyen, a matsayin wata hanya ta zamar da Xiaojin wuri mai kyan gani. Mutanen kauyen na kiranta da Sarauniyar Rose ko kuma Sakatariyar Rose saboda yabawa taimakon da ta yi musu.

A matsayin wurin dake yankin kan tudu mai tsawon kusan mitoci 3,000, kauyen Maoshui ya kasance mai karancin kasar noma, da rashin tsarin sufuri mai kyau.

A baya, matasa a Maoshui kan tafi neman aiki na wucin gadi a birane, inda suke barin gonaki ba tare da nome su ba. Sai dai, saboda tagomashin da ake samu daga noman Rose, rayuwar mutanen kauyen ta inganta.

Chen Wanghui ta ce, “Kauyen da a baya ke fama da talauci, yanzu ya kafa sabbin fitilun kan titi da shimfida sabbin tituna. Ana amfani da filayen gidajen mutanen kauyen wajen shuka Rose”.

A farkon shekarar 2006, Chen da mijinta suka kafa wani dakin cin abinci da Otel, wanda ya samar musu kudin shiga da kuma girmamawa daga mutanen kauyen.

Chen ta yi bayanin yadda ta ji nauyin taimakawa mutanen kauyen wajen samun kudin shiga ya rataya a wuyanta, musamman bayan ta gano cewa mafiya yawansu ba su da isasshen kudin tura ’ya’yansu makaranta ko zuwa asibiti.

Abu na farko da Chen ta yi bayan an zabe ta a matsayin daraktan kwamitin kula da harkokin kauyen a shekarar 2010 shi ne, gina sabbin tituna. Daga nan, sai ta fara laluben hanyoyin da za su taimakawa mutanen kauyen tsayawa da kafarsu.

Da farko, tunani hanyoyin da za ta bi wajen cimma burinta ya yi mata yawa, duk da cewa tana da yakinin cimma burinta.

A baya, kauyen Maoshui ya yi suna a matsayin kauye mai fama da talauci. Da kyar mazaunansa ke iya samun amfanin gona bayan shuka da girbin masara da dankali da alkama, wadanda a galibin lokuta aladun daji ke cinyewa.

Yayin wani rangadin duba tsirran da aladun daji suka lalata, Chen ta lura da wasu furannin Rose a gonakin, nan da na kuma ta fahimci cewa, furannin na iya tsirowa da kyau saboda ganyensu mai kaya. Baya ga haka, yadda Maoshui ke yanki mai tsawo da kuma rana mai karfi a yankin, ya sa shi dacewa da samar da ingantattun furannin Rose.

Chen ta yi nazarin abun da ta gani, daga bisani ta gabatar da shawarar fara noman furannin, inda mazauna kauyen da suka manyanta da masu bukata ta musamman suka shiga aka dama da su.

A shekarar 2012, Chen ta ziyarci manoman Rose a manyan yankuna 24 na larduna daban daban, inda ta neme su bayyana mata dabaru mafi inganci na noman Rose. Daga baya, ta yi nasarar shuka nau’o’i daban daban na Rose har guda 8 tare da wani nau’i na aure tsakanin Rose na daji da irin na Pingyin, na Lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.

Bayan wannan sabon nau’in Rose ya samu karbuwa a kasuwa, sai Chen ta sarrafa su zuwa miya da ganyen shayi, kuma ta ba wata masana’anta dake birin Lanzhou aikin matse man furen Rose.

Furanni daga kauyen Maoshui sun samu yabo sosai daga masana saboda ingancinsu, da kamshinsu na musamman, kuma ba sa dauke da warin maganin kashe kwari.

Saboda yanayi da kasa mai kyau, Maoshui ya yi wa sauran yankunan kasar Sin zarra a fannin raya kasuwancin furannin Rose, musamman a bangaren zuba jari da samun riba.

A cewar Chen, yara da manya duka na iya girbin furannin Rose. Kuma a karkashin jagorancinta, wasu jami’an kauyen da mazaunansa, sun fara shuka furannin.

Baya ga wannan, Chen ta kafa wata kungiyar gama kai ta noman Rose, kuma ta hanyar kungiyar, ana sayen furannin daga manoma a kan farashin da ya dara na kasuwa a lokacin da ba na shuka ba. Haka kuma, Chen ta hada hannu da sassan gwamnati masu ruwa da tsaki wajen samar da manufofi da taimakon kudi daga gwamnati.

Saboda nasarar da Maoshui ya samu, Chen ta kara burinta, domin taimakawa karin mutane daga gundumar Xiaojin amfana daga noma da girbin furannin Rose. A yanzu, mutane daga kauyuka 40 a gundumar na noman Rose a filayensu domin samun karin kudin shiga.

Da taimakon Chen, wani manomi mai suna Yu Fuliang, mai bukata ta musamman, ya fara noman Rose a shekarar 2015. Ya samu yuan 3,700 kwatankwacin dala 529 daga sana’ar, bayan shekara ta zagayo. Yanzu yana da gonakin Rose 4, fadin kimanin kadada 0.27, kuma yana samun kudin shiga mai yawa da ya kai yuan 40,000, kwatankwacin dala 5,714 a shekara.

Yu ya ce, “noman Rose sana’a ce mai kyau ga mutane irina, dake yankin tsaunika, domin samun rayuwa mai kyau.”

A shekarar 2016, aka zabi Chen a matsayin sakatariyar reshen JKS a kauyen Maoshui. Bayan shekara ta zagayo, ta sayar da gidanta, ta kuma ranci kudi daga ‘yan uwa da abokai, ta kuma yi amfani da dukkan kudin da take adanawa, wajen gina wani dakin samar da kayayyaki daga furannin Rose.

Dakin mai fadin sama da murabba’in mita 4,000, ya samar da gomman kayayyaki daga furannin, wadanda ake matukar bukata a ciki da wajen kasar Sin.

Baya ga haka, Chen ta hada hannu da wani kamfani dake birnin Shenzhen, wajen samar da ruwan sinadarin kurkure baki da kayayyakin kwalliya.

Sansanin noman Rose da Chen ta kafa, ya zama wani ginshikin masana’anta ga gundumar Xiaojin, kuma ya taimaka wajen fitar da mazauna wurin daga kangin talauci. Alkaluma sun nuna cewa, kimanin iyali 1,200 masu fama da talauci da wasu iyalai 470 dake da masu bukata ta musamman, daga kauyuka 31, dukkansu sun fita daga kangin talauci ta hanyar noman furannin Rose.

Matsakaicin kudin shigar manoman Rose a shekara ya kama daga yuan 50,000, kwatankwacin dala 7,143 zuwa yuan 100,000, kwatankwacin dala 14,286. Chen ta ce, za ta yi kokarin hada noman Rose da raya masana’antar yawon bude ido a karkarar, domin inganta farfadowar kauyen da samar da karin hanyoyin samun kudin shiga ga mutane.

Gundumar Xiaojin ta gina yankunan nune-nunen Rose da kwarin Rose da wuraren gwaji na gani da ido, wadanda fadinsu ya kai hekta 7.3, kuma gundumar ta kafa wani tsarin masana’anta da ya kunshi noman Rose da sarrafawa da sayarwa da wajen bude ido da gwaji da koyarwa da kuma nazarin kimiyya.

Wannan dabarar raya harkar bude ido ta musamman, wadda ta hada da ziyartar tsoffin wuraren tarihi da kallon furannin Rose da dandanon ganyen shayi, ya zama wani sabon kuzari dake ingiza raya harkar bude ido a yankin karkara.  

Ta ce a matsayinta na jami’ar kauyen, kara gudanar da muhimman ayyuka da jagorantarsu yayin da suke kokarin inganta rayuwarsu, nauyi ne da ya rataya a wuyanta.

“Ban taba tsammanin noman Rose zai kai kauyenmu kan tafarkin ci gaban tattalin arziki ba. Na yi amanna cewa, a nan gaba, kauyenmu zai haskaka kamar furannin Rose”, cewar Chen Wanghui.(Kande Gao)