logo

HAUSA

Sojojin Amurka sun yi amfani da motocin dakon mai 45 wajen satar man fetur a Syria

2023-07-31 11:26:52 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Syria na nuna cewa, sojojin kasar Amurka dake kasar Syria ba bisa doka ba, sun yi amfani da motocin dakon mai guda 45 wajen satar man fetur daga wurin hakar mai a arewa maso gabashin kasar Syria, zuwa sansanonin sojan Amurka dake kasar Iraqi jiya Lahadi

Haka kuma, majiyoyin cikin gida sun ce bayan da ayarin motocin dakon mai sun bar kasar, sojojin Amurka sun yi amfani da ayarin motoci da motoci masu dauke da na’urorin sanyaya abinci gaba daya guda 50 wajen jigilar wasu kayayyakin amfanin gona daga kasar ta haramtacciyar hanya ta kan iyaka dake Walid.

A halin yanzu, sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Syria ba bisa doka ba, sun mamaye galibin yankunan dake arewa masu gabashin kasar Syria, kuma sun hada kai da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar domin satar albarkatun Syria akai-akai, lamarin da ya haddasa karin barazanar jin kai a kasar. (Maryam)