logo

HAUSA

Kamata ya yi baligai su yi barcin awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana

2023-07-31 15:51:50 CMG Hausa

Kwanan baya, wasu masu ilmin likitanci na kasar Sin sun ba da shawarar cewa, ya kamata baligai su rika yin barci na tsawon awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana. Haka kuma ya dace su rika yin abubuwan da suka saba yi ta fuskar yin aiki da hutawa, su kuma kyautata tunaninsu, idan kuma sun gamu da matsalar barci, to, su je asibiti don ganin likita a kan lokaci.

Abubuwan da aka tanada cikin shirin ayyuka na shekarar 2019 zuwa 2030 dangane da kiwon lafiyar al’ummar kasar Sin sun nuna cewa, yanzu matsakaicin tsawon lokacin da baligan kasar Sin suke dauka wajen yin barci ya kai awoyi 6.5 a kowace rana. Saboda haka shirin ya fito da manufar kara adadin zuwa awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana daga shekarar 2022 zuwa 2030.

Gao Fu, darektan cibiyar kandagarki da dakile cututtuka ta kasar Sin ya yi bayani da cewa, yanzu matsalar barci da cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da matsalar barci suna kara addabar mutanen kasar Sin. Wasu mutane fiye da miliyan 400 suna fama da matsalar barci a nan kasar Sin. Kuma kusan kaso 60 cikin 100 na kananan yara da matasa ne ba sa samun isasshen barci. Sabon nazari ya nuna cewa, matsalar karancin barci na dogon lokaci yana kara barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini, ciwon damuwa, ciwon sukari da matsalar kiba, tare da haifar da rashin fahimta, cutar mantuwa, da lalata tsarin garkuwar jiki. Akwai cututtuka iri-iri fiye da 80 da suke da nasaba da matsalar barci.

Masana sun yi nuni da cewa, akwai shaidu ta fuskar kimiyya dake nuna cewa, dole ne baligai su yi barci na tsawon awoyi 7 zuwa 8 a kowace rana, lamarin da yake amfanawa lafiyar mutane. Amma sakamakon dalilai da dama, ya sa tsawon lokacin barci yake raguwa ga yawancin mutane. Yawan mutanen da ke fama da matsalolin barci, musamman ma matsalar karancin barci, yana karuwa.

Mene ne dalilin dake hadasa haka? Saboda mutane na kara fuskantar babban matsin lambar yin takara mai zafi sakamakon ci gaban tattalin arziki da zamantaker al’ummar kasa. Bayan haka kuma, wasu ba sa rayuwa ta hanyar da ta dace. Alal misali, suna sabawa da yin barci a makare da dare, suna matukar sha’awar yin wasa da wayar salula. Har ila yau tsufa na tsananta matsalar barci.

Masana sun nuna cewa, akwai bukatar daidaita matsalar barci baki daya ta hanyar kimiyya. Kowa da kowa na iya kare kansa daga matsalar barci ta hanyar yin rayuwa yadda ya kamata. Amma idan matsalar barci ta shafi ayyuka da zaman rayuwar yau da kullum, to, ya fi kyau a je asibiti don ganin likita a kan lokaci.

Sabili da haka ne gwamnatin Sin ta karfafa gwiwar hukumomin likitanci su ba da hidimar barci, alal misali, ba da jagora kan yin barci ta hanyar kimiyya, a kokarin rage abkuwar matsalar barci ga baligai. (Tasallah Yuan)