Putin: Shawarar Afrika Ta Warware Rikicin Ukraine Ta Yi Daidai Da Shirin Wanzar Da Zaman Lafiya Na Kasar Sin
2023-07-30 16:33:59 CMG Hausa
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, shawarar wanzar da zaman lafiya game da rikicin Ukraine da Afrika ta gabatar, ta yi daidai da tanade-tanaden shirin wanzar da zaman lafiya da kasar Sin ta gabatar.
Fadar Kremlin ta ruwaito shugaba Vladimir Putin na bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin tawagogin kasashen Afrika game da rikicin Ukraine, inda ya ce wasu kasashen yamma ne suka ingiza rikicin na Ukraine, wadanda suka shafe shekaru da dama suna tsara hanyoyi daban daban na ingiza yaki.
Da yake jawabi, Cyril Ramaphosa, shugaban kasar Afrika ta Kudu kuma daya daga cikin wadanda suka gabatar da shawarar, ya ce abun farin ciki ne jin cewa shawarwarin da suka gabatar sun yi daidai da na sauran bangarori, musamman kasar Sin.
Ya ce hakika a yanzu rikicin ya shafe su kai tsaye, yana mai cewa ana samun matsaloli a bangarori da dama, ciki har da wadatar abinci.
Ya kara da cewa, sun yi ammana cewa, farfado da zaman lafiya zai amfanawa bil Adama da ma al’ummun kasashen Rasha da Ukraine.
Wata tawagar rajin wanzar da zaman lafiya ta nahiyar Afrika ta ziyarci Ukraine da Rasha a watan Yunin bana, domin ingiza sasanta rikicin Ukraine. (Fa’iza Mustapha)