logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi kira da a dagewa wasu kasashen Afirka takunkumai

2023-07-29 16:16:19 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga kwamitin tsaron majalissar da ya dagewa wasu kasashen Afirka takunkuman da ya kakaba musu, ko sa samu zarafin kare fararen hula yadda ya kamata.

Geng Shuang, wanda ya yi kiran yayin zaman kwamitin tsaron MDDr game da ayyukan wanzar da zaman lafiya, mai nasaba da kare fararen hula a jiya Juma’a, ya ce kasashen da tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD ke aiwatar da ayyuka a cikinsu, su ne ke da alhakin kare fararen hula, don haka ya kamata tawagogin majalissar su tallafawa kasashen, wajen shawo kan kalubalen tsaro, da ingiza kwazonsu na kare rayukan fararen hula.

Jami’in ya kara da cewa, takunkuman kwamitin tsaron MDD kan wadannan kasashe na Afirka, na dakile ikonsu na kare fararen hula. Don haka ya kamata a gaggauta dage su. Kaza lika Geng ya bukaci sassan kasa da kasa, da su karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka, su goyawa kasashen baya, wajen farfado da dogaro da kai a fannin kiyaye zaman lafiya. (Saminu Alhassan)