Tawagar daliban jami’ar Uganda na kammala shirin halartar gasar Chengdu
2023-07-28 15:05:34 CMG Hausa
Yayin da gasar daliban jami’o’in kasa da kasa da za a gudanar a birnin Chengdu na kasar Sin ke kara karatowa, dalibin ilimin injiniya a jami’ar Makerere ta Uganda Kenneth Mwambu, na kara azamar kammala shirin halartar gasar wasan badminton, karkashin tawagar kasar sa.
Mwambu mai shekaru 23 da haihuwa, ya ce yayin da wannan gasa ke karatowa nan da ‘yan kwanaki, suna ta maida hankali ga gyara kura-kurai da suke da su, da karfafa kwarewa.
Dalibin wanda ya bayyana hakan, yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida a wurin samun horo na Kalerwe, dake wajen birnin Kampala fadar mulkin Uganda, yana cikin tawagar ‘yan wasan badminton 7 dake cikin babbar tawagar mutane 40, ta daliban jami’o’in kasar Uganda, wadanda za su halarci wannnan gasa ta “FISU 2023”, wadda za a bude ranar Juma’a 28 ga watan nan na Yuli.
A cewar Mwambu, shirin da ya shafe lokaci yana yi domin shiga wannan gasa, alama ce ta jajircewa, duk da tarin kalubale da ‘yan wasan motsa jiki na kasashe masu tasowa ke yawan fuskanta. Bayan gudanar da horo mai tsanani na samun kwarewa, Mwanbu ya ce "Lokacin ina yaro, na kan yi fama da rashin lafiya. Mahaifiya ta ce ta rene mu, mu uku a wurin ta".
Tun daga shekarar 2016, lokacin da Mwambu ya fara buga badminton a makaranta, ya fuskanci wahalhalu na samun kayan wasa. Mahaifiyar sa ce ta rika taimaka masa da dan abun dake hannun ta.
Duk da haka, bisa dagewar sa, da mayar da hankali, Mwambu ya kai ga shiga tawagar kasar Uganda a shekarar 2021. Wannan dama ce da ta bude masa manyan kofofi na shiga gasannin kasa da kasa, ciki har da gasar kasashe renon Ingila da aka gudanar a shekarar 2022 a birnin Birmingham, da gasar kasashen nahiyar Afirka ta shekarar 2023.
Mwambu wanda ya taba yin atisaye a Indiya, ya ce ya kagu ya buga wasa a gasar birnin Chengdu, na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Mwambu ya ce "Daga hotuna da nake gani, ina hasashen ganin yanayi mai kayatarwa a wannan gasa, wadda za ta gudana a birni mai ban sha’awa da kyan gani. Na san kasar Sin ta kware wajen shirya wurare ta yadda za su kayatar, wanda hakan ke zaburar da shaukin gudanar da gasa mai burgewa".
Da zarar an bude wannan gasa, Mwambu na fatan shiga a dama da shi sosai, a wannan gasa ta kasa da kasa. Game da hakan, Mwambu ya ce "Buri na shi ne na yi iyakacin kwazo na. Bana zaton zan samu nasara cikin sauki. Na san cewa gasar cike take da kwararrun ‘yan wasa. Zan fi mayar da hankali ga wuce zagayen farko na gasar, har na kai iya inda kwazo na zai kai. Na jima ina samun horo domin tabbatar da ingancin wasa na, ta yadda zan yi takara sosai".
Bayan dan tattaki kadan daga inda Mwambu ke samun horo, akwai wani wuri mai suna Ntinda, inda dalibin koyon ilimin kimiyyar watsa labarai da shirye shirye, mai suna Emmanuel Kiwanuka ke samun horon linkaya. Kiwanuka yana ta kokarin inganta fasahar linkaya gabanin gasar Chengdu dake tafe.
Kiwanuka ya ce "Ina kwashe kwanaki 6 a duk mako ina yin atisaye, ina samun horo sau 2 a kullum, ina hutawa a ranar Lahadi kadai. Duk mako ina shan aiki mai tarin yawa. A yanzu, ina mayar da hankali ga inganta kwarewa ta, ina karya matsayin bajimta ta, ta yadda zan kai ga cimma babbar nasara". Dalibin ya kuma bayyana fatan kaiwa ga lokacin halartar wannan gasa dake tafe a Chengdu, wadda za ta ba shi zarafin haduwa da sauran ‘yan wasan motsa jiki daga sassan duniya daban daban.
A nasa bangare kuwa, Patrick Sebuliba, wanda ke rike da mukamin mataimakin shugaban tawagar kasar Uganda, wadda za ta halarci wannan gasa a Chengdu, ya ce kasar Sin ta zama abun misali a fannin shirya gasanni masu kayatarwa, kuma ta nuna kwarewa wajen ci gaba da zantawa, tsakanin mashirya gasar da dukkanin kasashe da yankunan da za su halarci gasar.
Sebuliba ya jinjinawa kwazon kasar sin, bisa yadda har kullum kasar ke yunkurin tallafawa fannin wasanni, yana mai ba da misali da yadda take samar da kayan horo, da wuraren horaswa a makarantun ta, inda matasa ke samun isasshen horo na zama kwararru a fannin wasannin motsa jiki. Sebuliba ya ce "Daga abun da na gani ta kafar bidiyo da hotuna, gasar birnin Chengdu za ta kayatar matuka. A namu bangaren, duk da kalubalen zabo ‘yan wasa da muka fuskanta, da kalubalen wuraren horaswa, da kayan wasa, ‘yan wasan mu sun shirya nunawa duniya kwazon su a wannan gasa dake tafe".
A bangaren sa kuwa, kocin Badminton na ‘yan wasan Uganda Freddieh Rellys Kirabo, cewa ya yi ko shakka ba bu, gasar birnin Chengdu za ta ilmantar. Ya ce "A matsayin mu na tawaga, mai kunshe da mai horaswa, da wakilan kasar mu, za mu koyi abubuwa da dama. Ina da kwarin gwiwar cewa za mu samu karin kwarewa matuka bayan gasar".