logo

HAUSA

Gwamnatin Syria: Takunkuman kasashen yamma sun haifar da matsalar jin kai a Syria

2023-07-28 11:40:20 CMG Hausa

Ministan kula da harkokin wajen Syria, Faisal Mekdad ya ce takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakkabawa kasarsa, sun jefa al’umma cikin yanayin matsalar jin kai.

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya ruwaito ministan na bayyana haka ne yayin wani taro da wakilan wasu hukumomin MDD da na kasa da kasa dake Syria, inda ya bayyana matsanancin yanayi da wahalhalun da al’ummar Syria ke fuskanta.

Da aka tabo batun ’yan gudun hijira na kasar, Faisal Mekdad ya yi bayani game da kokarin da gwamnatin kasar take na mayar da su gida cikin mutunci da aminci. (Fa’iza Mustapha)