logo

HAUSA

Putin: Rasha na son inganta alaka ta fannoni daban-daban da Afirka

2023-07-28 11:41:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, kasar Rasha na da matukar sha'awar zurfafa huldar kasuwanci da zuba jari da kuma harkokin jin kai da Afirka a fannoni daban-daban, da za ta biya bukatun dukkan kasashen duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin bude taron kolin tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka a cikin tsarin taron kolin Rasha da Afirka karo na biyu.

Ya kara da cewa, kasashen yammacin duniya suna kawo cikas ga samar da hatsi da takin kasar Rasha, amma saboda “munafurci” suna zargin Moscow da haifar da matsalar abinci a duniya.

Putin ya ce Rasha za ta ci gaba da samar da hatsi ga kasashen Afirka.

Har ila yau, ya jaddada muhimmancin bunkasa hadin gwiwar hada-hadar kudi, inda ya kara da cewa, yana da matukar muhimmanci a sauya sheka zuwa yin amfani da kudaden cikin gida na kasashe wajen gudanar da harkokin cinikayya da juna, wanda zai saukaka biyan kudade tsakanin kasashe duk da takunkumin daga tsarin kasashen yammacin duniya. (Yahaya Babs)