Mene ne ainihin makasudin ziyarar manyan jami’an Amurka a yankin kudancin tekun Pasifik?
2023-07-27 20:32:03 CMG Hausa
Jiya Laraba 26 ga wata, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya halarci bikin kaddamar da sabon ofishin jakadancin Amurka dake kasar Tonga, al’amarin da ya zama karo na farko da aka bude irin wannan ofishin jakadanci, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya shekaru 51 da suka gabata. A dai jiyan, ministan tsaron Amurka Lloyd Austin, ya ziyarci kasar Papua New Guinea, kana jami’an Amurkar biyu za su hadu a kasar Australiya, don halartar shawarwarin shekara-shekara da ake kira “2+2” tare da bangaren Australiya. A ‘yan shekarun nan, Amurka na kara mayar da hankali ga halartar harkokin yankin kudancin tekun Pasifik.
Ba’a dai taba ganin irin wannan kwazo na Amurka a wannan yanki cikin shekaru da dama da suka gabata ba. Amma abun tambaya shi ne, yaushe ne Amurka ta sauya manufar ta game da wannan yanki?
A zahiri take cewa a ‘yan shekarun nan, kasar Sin na kara hada kai tare da kasashe tsibiran tekun Pasifik bisa tushen girmama juna, al’amarin da ya samu maraba sosai daga gwamnatoci gami da al’ummun kasashen, yayin da ita Amurka ke nuna damuwa sosai, har ma ta sauke girman kai, da rashin kulawar da take nuna ga yankin, kana ta fara tura wasu manyan jami’anta don ziyartar wadannan kasashe, da yi musu alkawarin samun babban tallafi.
Amma mene ne ainihin makasudin Amurka na yin hakan? Jaridar Washington Post ta nuna cewa, makasudin shi ne shawo kan muhimmiyar rawar da kasar Sin ke kara takawa a wannan yanki. Kana, akwai manazarta da suka bayyana cewa, Amurka na son lalata moriyar kasar Sin a yankin kudancin tekun Pasifik, tare da kawo tsaiko ga hadin-gwiwarta da kasashen yankin.
Amurka ta kirkiro abun da take kira “barazana daga kasar Sin”, da zummar tilastawa kasashen yankin kudancin tekun Pasifik gudanar da harkokinsu bisa ra’ayinta, amma ta raina kudirin kasashen na tsayawa neman ci gaba cikin ‘yanci. Kamar dai yadda firaministan tsibirin Solomon, Manasseh Sogavare ya ce, “babu wani abun da zai iya hana hadin-gwiwar sada zumunta tsakanin kasarsa da kasar Sin.” (Murtala Zhang)