logo

HAUSA

FISU: Daliban jami’o’in Nijeriya na fatan cimma nasarori a Chengdu

2023-07-27 07:36:55 CMG Hausa

Masu kallonmu, a ranar Jumma’a ta wannan mako ne, za a fara gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa ta lokacin zafi karo na 31 a birnin Chengdu dake kudu maso yammacin kasar Sin, kuma, ’yan wasa na kasar Nijeriya suna fatan cimma nasarori a gasar ta wannan karo.