logo

HAUSA

Ci gaba da musaya zai ingiza kyautatuwar aminci tsakanin Sin da Amurka

2023-07-27 15:57:49 CMG Hausa

Yayin da manyan jami’an Sin da na Amurka ke kara bunkasa musaya tsakaninsu, masharhanta na kallon hakan a matsayin hanya mafi dacewa, ta farfado da alakarsu, tare da kawar da tarnakin dake mayar da hannun agogo baya, a wannan muhimmiyar dangantaka mai tasiri ga su kansu kasashen biyu, da ma sauran sassan duniya baki daya.

A baya bayan nan, mamban hukumar siyasa, kana direktan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin kolin JKS, Wang Yi ya gana da sakataren wajen Amurka Antony Blinken a birnin Jakarta, a gefen taron ministocin kasashe mambobin kungiyar ASEAN, inda suka yi musaya don gane da batutuwan dake jan hankalin kasashensu. Kaza lika kafin hakan mista Blinken ya ziyarci kasar Sin a watan Yuni da ya gabata, baya ga ziyarar da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen ta kai kasar Sin, tare da zantawa da firaministan kasar Li Qiang, da ma mataimaki sa He Lifeng a farkon watan nan na Yuli. Har ila yau, wakilin musamman na shugaban kasar Amurka game da sauyin yanayi John Kerry, shi ma ya ziyarci kasar Sin ba da jimawa ba, inda ya tattaunawa da manyan jami’an kasar game da batutuwan da suka jibanci farfado da hadin gwiwar sassan biyu kan batun sauyin yanayi.

Ko shakka babu, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, da tasiri ga kyautatuwar rayuwar al’ummunsu, da ma na sauran kasashen duniya baki daya, kamar dai yadda jami’an sassan biyu suka sha jaddadawa.

To sai dai kuma, kamar yadda muka sha gani, akwai ’yan siyasar Amurka da dama dake siyasantar da alakar kasarsu da Sin, suna yunkurin gurbata tarihin dangantaka, da gurgunta cudanyar Amurka da Sin. Irin wadannan ’yan siyasa burinsu shi ne lahanta moriyar kasar Sin, ta hanyar shafawa kasar bakin fenti.

Lallai yunkurin irin wadannan ’yan siyasa marasa hangen nesa, na iya yin tasiri ga tunanin Amurkawa da dama, wanda hakan ka iya haifar da kyama, ko kin jinin Sin a cikin gida, matakin da ka iya yin tarnaki ga warware sabanin ra’ayi ko mahangar kasashen biyu cikin sauki. La’akari da haka, muna iya cewa, irin wadannan ’yan siyasa na haifar da babbar illa ga alakar Sin da Amurka, maimakon su zamo wakilai na gari masu kokarin dinke baraka.

Bisa kimar alakar Sin da Amurka, da tasirinta ga ci gaban harkokin kasa da kasa, ya dace a yi watsi da ra’ayin tsirarun ’yan siyasar Amurka, masu kokarin gurgunta tafiya mai kyau tsakanin kasashen biyu. Kuma hanyar yin hakan ita ce Amurka ta nacewa biyayya ga ka’idoji, da sanarwar hadin gwiwa uku da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, kana Amurkan ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma sassan biyu su ci gaba da tuntubar juna, bisa martaba moriyar juna, da kiyaye kimar manyan batutuwan dake jan hankalin su. (Saminu Hassan)