logo

HAUSA

Karancin barci kan haddasa teba

2023-07-26 11:09:40 CMG Hausa

 

Masu karatu, ko kuna fama da karancin barci? Wani sabon nazari ya nuna mana cewa, wadanda ba sa samun isasshen barci su kan yi teba, wanda hakan ka iya zai illanta lafiyarsu.

Wata tawagar kasa da kasa karkashin shugabancin kwalejin Imperial dake birnin London sun tattara bayanan lafiyar baligai dubu 5 da dari 1 da 51. Matsakaicin tsawon shekarun wadannan mutane ya kai 37 a duniya, rabinsu mata ne. Haka kuma dukkansu sun shiga binciken da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 2011 da 2013 dangane da lafiya da abubuwa masu gina jiki, sun kuma amsa tambayoyi dangane da barci. Masu nazarin sun yi amfani da na'urar daukar hoton sassan jiki na X-ray don kara gano kibar da ke akwai a cikinsu.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, matsakaicin tsawon lokacin barci na wadannan mutane bai kai awoyi 7 a ko wace rana ba.

Ta la’akari da shekarunsu na haihuwa, kabila, mizanin BMI, yawan kibar da suke da ita, inganci da matsalar barci da suke fama da ita, da dai sauransu, masu nazarin sun gano cewa, tsawon lokacin barcinsu yana raguwa, sai yawan kibar da ke akwai a kewayen kayayyakin ciki yana karuwa, musamman ma maza.

Kibar da ke akwai a kewayen kayayyakin ciki, tana illanta lafiyar dan Adam. Ta kan kara wa mutane barazanar kamuwa da cutar hawan jini, matsalar kiba, da wasu cututtukan da ke shafar yanayin sarrafa sinadaran jiki.

Masu nazarin sun yi hasashen cewa, kasa yin barci isasshe ya sanya wasu sassan kwakwalwar mutane gaza yin aiki yadda ya kamata, hakan kan sa mutane cikin damuwa. Haka kuma, kasa yin barci isasshe ya sanya mutane kara cin abinci.

Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, nazarin da suka gudanar, ya fito da sabbin shaidu game da kasancewar wata alaka a tsakanin kasa yin barci isasshe da kuma karuwar kiba a jikin dan Adam. Amma duk da haka sun yi nuni da cewa, akwai bukatar ci gaba da nazarin nasu, a kokarin gano yadda tsawon lokacin barci ya yi tasiri kan yawan kibar da ke akwai a kewayen kayayyakin cikin dan Adam, da kuma dalilin da ya sa hakan. (Tasallah Yuan)