logo

HAUSA

Maganar ’yanci a Amurka Tatsuniya ce

2023-07-26 17:36:48 CMG Hausa

Wani sabon rahoto da asusun kula da yawan al’umma na MDD UNFPA ya fitar a kwanakin baya, ya nuna yadda mata da ’yan mata masu asali daga Afirka suka dade suna fuskantar wariya a fannin kula da lafiya a Amurka, lamarin da ya jima yana jefa rayukansu cikin hadari musamman a lokacin haihuwa.

Rahoton na UNFPA ya kuma bayyana cewa, matan da lamarin ke shafa na gamuwa da kalubale ta fuskar wayar da kai game da kiwon lafiya, da rashin lura da su yayin tsara manufofi, da hidimomin da ake bukata yayin haihuwa. Amma a mafi yawan lokuta mahukuntan na Amurka kan fake da zama masu kare hakkin da-Adam. Wannan shi ne an bar Jaki ana dukan Taiki

Bugu da kari, rahoton ya yi nuni da cewa, sau da yawa ana cin zarafin mata ’yan asalin Afirka ta hanyoyin hantara da muzgunawa ta zahiri, kana a kan hana su damar samun ingantacciyar kulawa, ko hana su magungunan kashe radadin ciwo.

Sakamakon hakan a cewar rahoton, wannan rukuni na mata kan gamu da matsaloli, da hadurra yayin goyon ciki, ko jinkirin samun kulawa a asibiti, wanda hakan kan kai wasu ga rasu rayukansu. Tambayata it ace a ina ’yancin da wadannan bayin Allah ke da shi na samun kulawar lafiya da ma kare hakkinsu?

Bugu da kari, a wuraren da ake da cikakkun alkaluman bayanai na abubuwan dake faruwa, an lura cewa akwai wagegen gibi tsakanin adadin mata bakaken fata dake mutuwa sakamakon haihuwa, idan an kwatanta da takwarorinsu fararen fata musamman a kasar Amurka, inda kiyasin mata bakaken fata daka iya rasa rayukansu yayin haihuwa, ya ninka na takwarorinsu fararen fata har sau 3.

Wannan ya kara nuna cewa, ikararin ’yan siyasar Amurka na ’yancin da ’yan kasar ke da shi a dukkan fannoni, tatsuniya ce kawai. (Ibrahim Yaya)