logo

HAUSA

Ziyarar likitoci Sinawa a Saliyo za ta ceci rayukan dimbin mata

2023-07-25 16:54:40 CMG Hausa

Birnin Freetown na Saliyo ya karbi manyan baki a jiya Litinin, wato tawagar likitocin kasar Sin, da za su taimakawa kasar yaki da cutar sankarar bakin mahaifa.

Sankarar bakin mahaifa, cuta ce da ta zama abar tsoro a tsakanin mata la’akari da yadda take wahalar da su da kai wa ga asarar rai a karshe. A cewar hukumar lafiya ta duniya, a shekarar 2020 kadai, cutar ta yi sanadin mutuwar mata 342,000 daga cikin kimanin 604,000 da aka yi kiyasin sun kamu da ita a shekarar a duk fadin duniya. Kuma kaso 90 cikin dari daga cikinsu, mata ne na kasashe masu matsakaici da karancin kudin shiga.

Likitocin za su gabatar da kwarewarsu a fannonin bincike da kula da gano cutar ta sankarar bakin mahaifa, tare da horar da takwarorinsu na kasar.

Irin wadannan tallafi da kasar Sin kan bayar ga kasashen Afrika a kai a kai ne dalilin da a koda yaushe na kan kira kasar a matsayin wadda ta san ya kamata kuma sahihiyar aminiya ga kasashen Afrika. Har kullum taimakon kasar Sin ga al’ummar Afrika, taimako ne irin na ’yan uwantaka, na sanin ciwon dan uwa, haka kuma taimako ne na kai tsaye da mutane za su amfana da shi. Zuwan likitocin, tabbas ba karamin taimako zai bayar ba, wajen ceton dimbin rayukan mata da ma karfafawa matan gwiwar zuwa ana duba su tun kafin cutar ta ci karfinsu.

Baya ga haka, yadda tawagar likitocin suka tashi musamman suka zuwa Afrika, zai kara zaburar da mahukuntan nahiyar wajen kara kula da lafiyar mata. Wani abu dake burge ni da kasar Sin shi ne, baya ga mayar da hankali kan kulawa da jama’arta, tana bayar da muhimmanci na musamman ga lafiyar mata. Tuni ta dauki dabarun yaki da wannan cuta mai kisa ta hanyar gudanar da bincike da kulawa, har da samar da rigakafi ’yar kasa.

Hakika akwai dabaru da darussa da dama da likitocinmu na nahiyar Afrika za su iya koya daga takwarorinsu Sinawa. Fatan ita ce, kwalliya za ta biya kudin sabulu, kana kasar Sin ta fadada wannan taimako zuwa sauran kasashen nahiyar domin ceton karin rayuka. (Fa'iza Mustapha)